A Zariya: Ziyarar shugaban kasa, matsala ga al’umma -Kansilan Tukur – Tukur

Ziyarar shugaban kasa

Ziyarar shugaban kasa

Tura wannan Sakon

Isa A. Adamu Daga Zariya

Tun daga ranar da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kawo ziyarar ganin ayyukan da gwamnatin jihar Kaduna ta yi, matsalolin buge yara a sabbin hanyoyin da aka yi ya zama ruwan dare a sassan karamar hukumar Zariya, musamman a kan sabbin hanyoyin da gwamnatin jihar Kaduna ta yi’’ Bayanin haka ya na kunshe a cikin jawabin da kansilar gundumar Tukur – Tukur.

Alhaji Muhammad Ibrahim ya yi a lokacin da ya ke gabatar da kuduri da kuma kke – koken al’ummar gundumarsa da sauran al’ummomi, na tun daga ranar da aka cire tuddan da aka yi a sabbin hanyoyin, a dalilin zuwan shugaban kasa, kamar yadda aka bayyana a baya, a duk rana, a cewar kansilan, sai ma su motoci da kuma Babura sun buge yara, musamman da safe, a lokacin da yaran ke kokarin zuwa makarantunsu.

Alhaji Muhammad ya ci gaba da cewar, kafin zuwan shugaban kasa Zariya, duk guje – gujen da ma su abubuwan hawa suke a wadannan hanyoyi, a dalilin wadannan tuddai, ba a jin matslolin da aka ambata, sai bayan cire wadanan tuddai da aka ambata.

A kan haka, kansilan ukur – Tukur, ya yi kira ga gwamnatin jihar Kaduna ta duba wannan matsalar da ta addabi daukacin da gidajensu ke kan sabbin hanyoyin da gwamnatin jihar Kaduna ta yi, musammam, hanyar da ta tashi daga Tukur – Tukur zuwa Tudun Jukun zuwa PZ da wadda ta tashi daga Kofar Doke zuwa Kwarbai zuwa Unguwar Katuka, Zage Zage zuwa Kwanar matasa a Unguwar Lalli birnin Zariya.

Sauran hanyoyin da aka cire wadannan tuddai, da cire su ya zama babbar matsala ga al’umma a karamar hukumar Zariya, sun hada da hanyar da ta tashi daga Bakin Kasuwar birnin Zariya zuwa Kaura zuwa Unguwar Kahu zuwa Kofar Galadima, a cewarsa, duk rana ana samun wannan matsala, da ya haifar da yara da manya da dama da ke jinyar raunukan da suka samu daga ma su guje – guje da abubuwan hawa, a kan hanyoyin da aka ambata.

A karshen jawabin da ya yi, ya yin gabatar da wannan kuduri, Alhaji Muhammad Ibrahim, Kansilan Tukur – Tukur, ya yi kira ga shugaban karamar hukumar Zariya, Injiniya Aliyu Ibrahim, da ya duba wannan babbar matsala da al’ummomin da aka yi wadannan hanyoyi a Unguwanninsu suke ciki, ya dauki duk matakan da suka dace, domin dawo da wadannan tuddai a wadannan sabbin hanyoyi da aka ambata, domin kawo karshen matsaloli.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *