Abdullahi Mahmud Gaya :Shekaru shida na jagoranci

Abdullahi Mahmud Gaya
Daga Ibrahim Umar
Kamar yadda kowa ya sani kowanne nagartaccen shugaba akwai wani kuduri da suke da shi mai kunshe da fikira da dattako a kan abinda suke da shi na buri, ko kuma wanda suke muradin aiwatarwa wajen gudanar da shugabanci nagari mai cike da alheri.
Cikin manyan ayyukan nagartaccen shugaba ya kasance mai kwarin gwiwa, nagarta, mayar da hankali, da fahimta cikin sauki a ayyukansa na jagoranci ko wakilci, shakka babu Alhaji Abdullahi Mahmud Gaya yana da dukkanin wata nagarta da ingancin shugabanci a matsayinsa na bawan mutane ko kuma ma’aikaci, wanda hakan ya ba shi damar gabatar da ayyukan da shirye shirye baya ga ayyukan madallah a wakilcinsa na farko da na biyu a zauren majalisar wakilan kasar nan a matsayinsa mai wakiltar kananan hukumomin Gaya, Albasu, da kuma Ajingi.
Tun a farkon zabensa a 2015 a matsayin sabon dan majalisa a zauren majalisar wakilai, ya mayar da hankali gaba daya wajen zuwa da sababbin tsare-tsaren wakilci, da kuma zama dan siyasa mai fa’ida da manufa a cikin takwarorinsa ‘yan siyasa.
Abdullahi Mahmud Gaya ya bukaci dukkanin takwarorinsa ‘yan majalisa su amince wajen sadaukar da rabin albashinsu zababbu a majalisar kasa, domin tallafa wa gwamnati kudaden da za ta gudanar da ayyukan ci gaba a lokacin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya karbi mulkin kasar nan 2015 babu kudade, domin ganin an farfado da hanyoyin magance masarsarar tattalin arziki da ya addabi kasar nan dama duniya baki daya a wancan lokaci.
Tun a farkon wakilcinsa ga ‘yan mazabarsa a ranar 9th ga watan Yuni 2015, lokacin majalisa ta 8 ba tare da bata lokaci ba, gwanin dan majalisar ya fara gudanar ayyukan raya mazabunsa da zuwa da salo da tsari mai nagarta wanda ba’a taba gani a wannan yanki ba,.
Mahmud Gaya ya ci gaba da gabar da kudirai da yake da sun a sabbin tsari da ya zama jakada nagari wajen kirkirar tsarin Gaya, Albasu, Ajingi sabuwa. Al’ummar yankin Gaya, Albas, da Ajingi shaida ne dukkanin wakilan da aka zaba kafin Abdullahi Mahmud Gaya daga shekarar 1999-2015 babu wani wakilin da ya gudanar da tsari kamar sa, domin yanayinsa na tafiya da zamani da kuma abinda al’ummarsa ke muradi.
Tun bayan dawowar mulkin dimukuradiyya a 1999, babu wani dan majalisa da ya bude office a mazabu, tare da sanya kayan gudanarwar ofishoshin a dukkanin mazabun yankinsa sai Hon Gaya, kuma wannan ya zo ne daga lokacin da aka rantsar da shi, kuma ko a yanzu wadannan ofisoshi na ayyukansu kamar yadda aka sani, kuma ya alkawarta zai gudanar da wakilci ne tare da al’ummarsa, wajen ba su damar kawo bukatunsu ko shawarwarinsu a wajen gudanar da wakilci, da kuma bayyana irin aikin da suke so a inda suke so, domin shi a kullum bukatar al’ummarsa ita ce a gaba kuma wannan shi ne tsarinsa a duk lokacin da aka sanya hannu a kundin kasafin kasa tun daga 2015 da aka zabe shi zuwa wannan lokaci.
Lokacin da aka zabe shi a majalisa ta 8, Abdullahi Gaya ya yi amfani da kudin ayyukan mazabu domin gyaran makarantu, sanya kayan koyo da koyarwa, da kuma ingnta bangaren ilmi, domin a muradinsa ilimi shi ne tushe na kowacce rayuwa, a yanzu haka ana ci gaba da gogayya da yankin Gaya, Albasu da Ajingi a matsayin yankin da ya samu ci gaba da fuskar ilimi, wannan na daga cikin jajircewar dan majalisar su.
Sannan ya inganta bangaren lafiya, da samar da gadaje, da da magunguna da asibitocin mazabu domin rage radadin rashin lafiya ga al’umma, kuma an ce gani ya kori ji, domin a shekaru 5 da ya yi yana wakilci al’umma sun sani Mahmud Gaya ya samar da rijiyoyin bayar da ruwa na burtsatse fiye da 100, a kowacce mazabar da take a yankin, ya samar da fitulun tituna masu amfani da hasken wutar lantarki a kananan hukumomin uku da yake wakilta, ya samarwa da dubunnan matasa ayyukan yi, musamman wanda za su tsaya da kafafuwansu wajen basu horo na musamman ta bangaren sana’o’i da kuma taimaka masu wajen basu kayan aikin noman rani da na damun
Alhaji Abdullahi Mahmud ya samar wa da al’ummarsa musamman matasa ayyukan yi a wadansu ma’aikatun gwamnatin tarayya, musamman aikin soja, dan sanda, sojan sama, sojan ruwa, kumar haraji ta kasa, babban bankin kasa CBN, a hukumar samar da wutar lantarki, da kuma ma’aikatun daban-daban na jiha dana tarayya kuma wadannan a iya zangon wakilcinsa na farko ya samar da ayyukan.
Ya bai wa mata dubunnai tallafi da basu jari wanda za su gudanar da raywarsu ta yau da kullum, ta shirin AMG WOMEN ECONOMIC EMPOWERNMENT PROGRAM (WEEP) a bangarori daban-daban da ba su jarin dubu 20 kowannensu.
Ya rarraba kekunan dinki da dubu 5 a matsayin jari, samarwa matan keken saka musamman ga wadanda suka rasa mazajensu domin tallafa wa iyalansu, ya raba wa ‘yan jam’iyya da al’ummar mazabarsa babura domin tallafa masu saukaka sufuri, kumaya rarraba dakin sanyi domin yin sana’ar kankara ga matasan yankin da mata, sannan ya bayar da tallafin injin bar ruwa ga manoma domin inganta tattalin arzikinsu.
A shekara biyu da yayi a majalisa ta 9 ya gina azuzuwa uku-uku a yawan mazabun da ake da su a kananan hukumomi 3 na Gaya, Albasu, da kuma Ajingi, ya gina a makarantar sakandiren mata da ke garin Faragai, ya gina azuzuwa uku a garin makarantar sakandire ta Ajingi, ya gina a makarantar sakandiren dake garin Shagogo, ya gina a sakandiren mata da ke garin Chula, ya gina a makarantar sakandiren mata da ke garin Dagagi, ya gina a sakandiren mata da ke garin Gamarya, ya gina a makarantar Technical da ke garin Kademi, ya gina a makarantar Malamawa Primary, ya gina a makarantar sakandiren da ke garin Tsangaya, ya gina a makarantar sakandiren mata dake garin Karar Dagagi kuma dukkaninsu an kammala. Kazalika ya samar da fanfan samar da ruwa a garin Kademi, da Tsangaya domin saukakawa al’ummar yankin wajen samun ruwan amfanin yau da gobe.
A bangaren abubuwan da su ka shafi mata ma ya rarraba wa fiye da mata 1,500 tallafin Naira 20,000 kowacce, inda kuma aka horar da mata 500 yadda ake kiwon awaki na zamani tare da ba su tallafin Naira 20,000, ya dauki nauyin koyar da mata fiye da 600 yadda ake kiwon kaji na zamani.
Ya bayar da tallafin magunguna ga karamar hukumar Gaya biyo bayan bullar ibtila’in cutar amai da gudawa a yankin, ya gina ajujuwan karatu a mazabu guda 23 daga cikin mazabu 30 da mu ke da su a kananan hukumomi guda 3 da mu ke wakilta wanda za mu kaddamar da su nan ba da dadewa”
Ya bai wa kowanne shugaban jam’iyyar APC da ke kananan hukumomin Albasu da Gaya da kuma Ajingi mota, gyarawa da samar da transformer domin al’ummarsa su samu saukin rayuwa.
Wannan ya nuna cewa, Alhaji Mahmud Gaya yaan daga cikin ‘yan majalisar da ko shakka babu ya zama zakaran gwajin dafi, domin ya a zangonsa na farko ya gudanar da ayyukan da ya taba talaka kai tsaye, ga wa’adinsa na biyu ma cikin shekarar farko an ga rawar da ya taka, kuma hakan ya nuna al’ummarsa sun amince da irin wakilcinsa, kuma yana bai wa al’ummarsa dama su tattauna da shi, domin sanin matsalarsu da magance masu duk wata damuwarsu a kowanne mako yana halartar ofishinsa domin karbar koken al’ummarsa.
Sannan yana tallafa wa dalibai domin gudanar da ilimi mai nagarta wajen biya musu jarrabawar karshe ta makarantar sakandire, watau NECO da WAEC, a yankunan kananan hukumomi uku da yake wakilci, kuma ya siya tare da rarraba form din jarrabawar UTME cikin shirinsa na AMG EDUCATIONAL SUPPORT PROGRAMME (ESP), dan majalisar tarayya mai wakiltar kananan hukumomi Gaya, Albasu da kuma Ajingi a majalisar wakilai ta kasa Alhaji Abdullahi Mahmud Gaya.
AYYUKAN DA SHUGABAN MAJALISARWA KILAI NA KASA YA BASHI
Cikin nagarta da kuma kwarewar aiki Gaya ya samu kansa a shugabancin kwamitin kar ta kwana domin bincikar badakalar kudi Naira biliyan 500, wanda za’a biya kungiyar masu kasuwancin man fetur, PPMC kuma kwamitinsa ya gudanar da aiki cikin salon a kwarewa, kuma an samu nasarar mayarwa da gwamnati biliyoyin kudade ta dalilin kokarinsa. Bayan waccan nasara da ya samu shugaban majalisar wakilai ya sanya shi a cikin kwamitin mutane 16 da za su tattara bayanan yadda za’a inganta harkokin tattalin arziki, da hanyar fita daga cikin matsin masharsharar tattalin arzikin da ya addabi kasa, kuma kwamitin ya yi kokarin tallafa wa kasar nan, wajen zama na musamman ta bangaren masu ruwa da tsaki, da suka hadar da kungiyar kwadago, kungiyoyin farar hula, da kungiyoyin ‘yan kasuwa da makamantansu, kuma an samu nasarar da ake bukata wajen fita daga matsin tattalin arziki