Abdulwahab Ta-karaye ta yaye mahaddata 5

Abdulwahab Ta-karaye ta yaye mahaddata 5

Abdulwahab Ta-karaye ta yaye mahaddata

Tura wannan Sakon

ISA A. ADAMU Daga Zariya

A ranar Lahadin da ta gabata, garin Karaye da ke jihar Kano ta yi cikar baka da al’umma da suka fito daga sassan ji­har Kano da wajen jihar, do­min shaida kammala haddar Alkur’ani mai girma na dal­iban makarantar ALBDUL­WAHAB LILL TAHFIZIL KUR’AN TORANKAWA, da taron walimar ya gudana a harabar makarantar da ke garin Karaye.

Wannan taro ya kuma sami halarta tare das a al­barkar mai martaba Sarkin Karaye Alhaji Dokta Ibra­him Abubakar na daya da shugaban karamar huku­mar Karaye Alhaji Balarabe Isyaku da wanda ya assasa makarantar Alhaji Bala Al- Belo da kuma wasu fitattun malaman addinin musulunci da suke ciki da wajen kara­mar hukumar Karaye.

Tun farko a wa’azin da ya gabatar a wajen walimar fitaccen malamin addinin musuluncin nan da ke Kano Shekh Malam Tijjani Bala Karawi,ya gabatar da wa’azi mai taken MUHIMMANCIN NEMAN ILIMI DA FALA­LAR ALKUR’ANI MAI GIRMA,

Shekh Bala Karawi ya bayyana cewar, babu wan­da ya san yawan falalar da ke tattatare da karatun Alkur’ani sai mai kowa mai komi, a nan ya kwadaitar da al’ummar musulmi das u tashi tsaye na rungumar karatun Alkur’ani mai gir­ma da kuma aiki da karatun da aka yi, duk wanda ya yi haka, a cewar Shehin mala­mi, mutum zai sami babban rabo a nan duniya da kuma gobe lahira.

Shekh Kalarawi ya ci gaba da tunatar da al’ummar musulmi cewar, Alkur’ani mai girma ya yi magana a kan Annabawa kafatan da kuma yadda Alkur’ani mai girma ya yi magana kan abin day a faru a tsakanin Iblis da Annabi Adamu da kuma Hauwa’u, a kwai bayan I da ke Al’kur’anin na gaban Ib­lis da dan Annabi Adamu sa­boda kamar yadda Alkur’ani ya bayyana, gaban ta samo asali ne daga uba, inda ya ce ya kamata al’ummar musul­mi su fahimta wannan gaba za ta ci gaba da gudana, har lokacin da Annabi Adamu zai shiga Aljanna shi kuma Iblis ya shige wuta a gobe.

Fitaccen malamin add­inin musulunci ya kuma bayyana yadda hassada ta samo asali, na yadda shaid­an ya yi wa Annabi Adamu Hassada, wanda kuma kamar yadda ya ce, Alkur’ani an yi magana ta yadda mai has­sada ke yin hassada da kuma yadda hassadar ke hallaka shi, musamman in bai bari ba.

A dai wa’azin da ya gab­ata, Shekh Tijjani Kalarawi, ya bayyana yadda Alkur’ani ya yi bayanin yadda aka fara kisan kai na farko a duniya a bayan kasa, yadda Kabila ya kashe dan uwansa Habi­lu, wannan Alkur’ani kuma a cewar Malam, shi ya bayy­ana wa al’ummar musulmi yadda ake rufe gawa, bayan mai rai ya mutu, kafin baya­nin Alkur’ani, danAdam bai san yadda zai yi da gawar dan uwansa ba, bayan ya mutu, a Alkur’ani ne, sai Al­lah ya aiko da wani fitaccen tsuntsu mai suna Hankaka, sai hankaka suka yi fada da dan uwansa, sai daya ya ka­sha daya, sai ya yi rami mai zurfi ya sad an uwan a cikin ramin da ya haka, a wannan lokaci dan Annabi Adamu ya ga yadda ake binne gawa.

Shekh Kalarawi ya tab­batar da cewar, Alkur’ani ne ke maganar jiya ya ke maga­nar yau da kuma bayanin gobe dalla – dalla, ta yadda `dan Adam zai san yadda zai gudanar da rayuwarsa daga zuwansa duniya ya zuwa ko­marsa ga wanda ya halicce shi.

Da kuma ya juya ga wan­da ya kafa wannan makaranta ta Alhaji Bala Alba Bello, ya yaba masa, kan wannan bab­ban aiki day a yi wa addinin musulunci da musulmi baki daya, ya kara da cewar, baa bin day a rage sai al’ummar da suke da halin mallakar abin duniya, su rika koyi da wannan bawan Allah, wajen amfani da dukiyarsu, domin ciyar da musulunci da ilman­tar da al’ummar musulmi baki daya.

A sa albarka da ya yi a wajen taron walimar, Mai martaba Sarkin Karaye Al­haji Dokta Ibrahim Abuba­ kar na farko, yaba wa Alhaji Alba Bello ya yin a amfani da dukiyarsa, wajen kafa wannan cibiyar neman ilimi a garin Karaye, kamar yad­da ya ce babu wanda ya isa ya san yawan wadanda ke amfana da wannan cibiya da kuma wadanda suka amfana da cibiyar shekaru da dama da suka gabata.

Mai martaba Sarki ya kuma yi kira da sauran al’umma da suke wannan masarauta ta Karaye da kasa baki daya, da su rika amfani da dukiyarsu, wajen ciyar da musulunci gaba ta kafa ma­karantu da kuma sauran cibi­yoyin neman ilimi a matakan neman ilimi daban – daban.

Ya kuma nuna matukar jin dadinsa da ya sami halar­tar wannan taro na Alkur’ani mai girma, musamman da kara jin fadakarwar da fit­accen malami Shekh Malam Bala Kalarawi ya gabatar a wajen taron da duk wanda ya halicci wannan taro, kamar yadda sarki ya ce ya sami babbar tsarabar da zai bayy­ana wa wadanda ba su sami halarta ba.

Mai martaba Sarkin Ka­raye ya kammala da kra ga iyayen yara da su kara tashi tsaye wajen kula da ilimin yaransu, ta sa su makarantun da za su sami ilimin addinin musulunci da ilimin zamani da kuma ilimin sana’a, wad­annan vangarorin ilimi su ne za su yi yaro jagora, a cewar Mai martaba Sarkin Karaye wajen zama nagari a cikin al’umma tun daga yau ya zuwa gobe.

Shi ko shugaban kara­mar hukumar Karaye Alhaji Balarabe Isyaku Karaye bay­an ya nuna farin cikinsa ga wanda ya kafa wannan cibi­ya, sai kuma y ace, majalisar karamar hukumar Karaye tan a da tsare – tsare da dama da suke aiwatarwa, domin talla­fa wa makarantun Islamiyya da kuma matasa da suke son ci gaba da neman ilimi.

Alhaji Isyaku Karaye ya kammala da cewar, wannan taro day a halarta, ya kara ma sa kwarin gwiwar kara tashi tsaye na ganin karamar hukumar Karaye ta ci gaba da tallafa wa makarantun Islamiyya da suke wannan yanki, domin su sami sau­kin fuskantar ilmantar da matasan karamar hukumar a cikin sauki.

A karshen wannan taro bayan an rarraba wa daliban da suka kammala haddar Alkur’ani mai girma kyau­tuttuka da takardun shaidar kammala haddar Alkur’ani mai girma a wannan ma­karanta, sai kuma wanda ya kafa makarantar Alhaji Bala Alba Bello ya nuna matukar jin dadinsa ga mai martaba Sarkin Karaye da ya halarci wajen walimar da kuma sau­ran al’umma daban – daban da suka fito daga ciki da wajen jihar Kano.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *