Abin da ya sa ‘yan sandan suka gayyaci Abduljabbar

DSP Kiyawa
A ranar Litinin 12 ga watan Yuli rundunar ‘yan sanda jihar Kano da ke Arewacin Nijeriya ta gayyaci Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara ya bayyana a gabanta, domin amsa wadansu tambayoyi kan kararsa da wani malamin ya kai.
Hakan na zuwa ne kwana biyu bayan kammala mukabala tsakanin Sheikh Abduljabbar da wasu Malaman Kano.
Sai dai kakakin ‘yan sandan jihar Kano, DSP Abdullahi Haruna Kiyawa ya ce, gayyatar da suka yi wa Malam Abduljabbar Nasir Kabara ba ta da alaka da mukabalar da aka yi da shi ko kalaman da malamin jihar ke zargin sa da yi.
“Wannan gayyata ba ta da alaka da wannan zama da aka yi, dama tun kafin a yi wannan zama akwai wadanda suka shigar da korafe-korafe a kansa, kuma an fara bincikawa, in ji Kiyawa.
DSP Kiyawa ya ce, har yanzu ana ci gaba da gudanar da bincike.
“Dama an sa ranar dawowa domin ci gaba da binciken, to kuma yau ce ranar kamar yadda aka sa a baya,” ya kara da cewa.
Wa ya kai karar Malam Abduljabbar?
Shugaban kungiyar Izala na Kano Sheikh Saleh Pakistan ne ya kai koke wajen ‘yan sanda kan zargin cewa Malam Abduljabbar na barazana ga rayuwarsa.
Ya shigar da koken ne a watan Fabrairu, kuma tun daga wancan lokaci Malam Abduljabbar kan je wajen ‘yaan sanda lokaci zuwa lokaci.
Gayyatar ta wannan karo ta zo ne tun ranar a Juma’a jajiberin mukalabala, amma Malam Kabara ya nemi uzuri cewa ga abin da ke gabansa yana kuma aikin hada littattafai, amma ya yi alkawarin zai kai kansa a ranar Litinin