Achraf Hakimi ya fitar da Moroko kunya

Tura wannan Sakon


Achraf Hakimi ya zama gwarzo bayan da ya yi cin fanareti mai kayatarwa da ya sa Moroko ta tsallake zuwa zagaye na dab da na kusa da na karshe a Gasar Cin Kofin Duniya.

Moroko ta yi nasara ne a kan Spaniya bayan fafatawar da aka shafe minti 120 ana yi – lamarin da ya kai har aka buga fanareti, inda Spaniya ta karar da uku a hannun mai tsaron ragar Moroko Yaccine Bounou.

Magoya bayan Moroko sun yi ta sowar nuna goyon baya tun farkon wasan duk da cewa Morokon ba ta taka rawar da ta dace tun fara wasan. Spaniya ce ta mamaye wasan inda ta dinga kai farmaki, yayin da ƴan wasan Moroko suka kasa suka tsare suka yi ta hana ƙwallon shiga ragarsu.

Ɓangarane kocin Spaniya Luis Enrikue ya yi ta ƙoƙarin fasa bayan Moroko a wani ƙoƙari da Dani Olmo ya dinga yi, inda ya buga wata ƙwallo da ta kusa shiga amma mai tsaron ragar Moroko ya kaɗe ta.

Moroko ta riga buga wasan ne a yanayin zari ruga kuma ya kamata a ce sun samu nasara tuna farkon wasan amma Nayef Aguerd ya buga ƙwallon da ka har ta fita waje, yayin da shi ma Noussair Mazraoui ya buga wata ƙwallon da za ta iya shiga raga wadda Unai Simon ya kwaso masa.

Dukka ɓangarorin biyu sun gaza cin ƙwallon a wasan, lamarin da ya sa aka tafi ƙarin lokaci na minti 30, inda ɗan wasan da Moroko ta sauya Walid Cheddira, ya samu kyakkyawar dama amma sai ya ɓarar da ita.

Yanzu Moroko za ta jira sai an kammala wasan Portugal da Switzerland an ga wacce za ta yi nasara, da ita ne za su fafata a zagaye na gaba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *