Adalci, dalilin tururuwa zuwa NNPP -In ji Danpass

Alhaji Gambo Dan-pass

Tura wannan Sakon

Daga Musa Diso

Wani fitaccen dankasuwa kuma jagora a tafiyar jam’iyar NNPP, Alhaji Muhammdu Gambo Danpass kuma Dan Saran Kano ya ce, adalci ne ya sanya jama’a suke tururuwa zuwa NNPP mai kayan marmari in ji Danpass.

Ya bayyana hakan a lokacin da yake zantawa da wakilin jaridar Albishir makon da ya gabata ya ce, tabbas adalci shi yake samar da jajirtaccen shugabanci kuma duk in da aka samu shugaba nagari kuma adali babu shakka za ka ga al’umma cikin annushuwar zaman lafiya da bunkasar tattalin arzikin kasa da kuma makamantansu.

Dan-saran Kano ya kara cewa, jam’iyar NNPP mai kayan marmari jam’iyya ce ta kowa da kowa da kuma masu son ci gaban al’umma da zaman lafiya da bunkasa tattalin arzikin kasa, kuma uwa uba jagoran jam’iyyar NNPP na kasa, Dokta Rabi’u Musa Kwankwaso fitacce ne a siyasar Nijeriya kuma jajirtaccen shugaba kuma babban burinsa a yanzu shi ne samar da tsaro, zaman lafiya domin ci gaban al’umma.

Dan Pass ya yi kira ga al’umma cewa, yanzu dama ta samu dabara ta rage ga mai shiga rijiya kuma jama’a su fito kwansu da kwarkwatarsu domin neman yancin su kuma su zabi jam’iyyar NNPP domin ita ce kadai jam’iyya a kasar nan wadda za ta kai jama’a tudun mun tsira.

Daga karshe, yaba wa shugaba kuma jogaran jam’iyyar NNPP na kasa, Dokta Rabi’u Musa Kwankwaso wajen jajircewarsa da ganin talakawa sun sami ‘yanci a Nijeriya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *