Addu ‘ar cikar shekaru 12 da rashin Limamin-canji: Masu akidar canji sun caccaki siyasar uban-gida

Alhaji Muhammadu Abu bakar Rimi,
Daga Mahmud Gambo Sani
Aranar Litinin da ta gabata, daruruwan magoya bayan limamincanji, Alhaji Muhammadu Abu bakar Rimi, suka hadu a babban masallacin Umar Bin Khattab da ke gab da gadar sama ta Dangi, cikin birnnin Kano domin yi masa addu’a ta neman Allah ya jaddada Rahama da jinkai gare shi.
Addu ‘ar cikar shekaru 12 da rashin Limamin-canji: Limamin na canji ya amsa kiran mahaliccinsa a ranar 4 ga watan 4, 2010.
Abin nufi yau shekarunsa 12 da rasuwa. Magoya baya da masu akidar siyasarsa da kuma ‘yan uwa da abokanan arziki sun taru domin tunawa da ranar da yi masa addu’a da kuma bitar irin ci gaban da ya samar ga ci gaban jihar Kano da siyasarta.
A taron tun da farko, sai da masana kuma hafizan Alkur’ani suka yi sauka daya, daga bisani hadiman masallacin suka jagoranci addu’o’ in nema wa tsohon gwamnan gafarar Ubangiji SWT
. Taron addu’ar ya wakana a karkashin shugabancin Alhaji Ibrahim Damisa, inda bayan addu’ar ya jagoranci wani bangare na mahalartan zuwa makabartar Farm Centre da ke unguwar Tarauni inda aka kara yi wa mamacin da sauran na kwance addu’o’in samun gafarar Ubangiji.
Duk da rashin bayar da sanarwar zaman cikin lokaci, mafi rinjayen masu akidar NEPU da PRP sun sami zarafin halarta. Daga cikin mahalartan, akwai Alhaji Aminu Abubakar Dabo da Alhaji Bala Muhammad Gwagwarwa da Farfesa Hafiz Abubakar (tsohon mataimakin gwamnan Kano) da Alhaji Bayero Gano da Alhaji Dauda Raula.
Sauran su ne, Alhaji Sule Chamber da Alhaji Tijjani Musa Wawu wanda ya wakilci Alhaji Inuwa Waya (mai takarar gwamnan Kano) da Alhaji Kabir Muhammad Gwangwazo, tsohon Manajan daraktan madaba’ar jaridun Triumph da Alhaji Kyauta Adamu, tsohon mataimakin shugaban majalisar birnin Kano da Kwamared Aminu Sa’ad Beli da kuma Alhaji Yahuza Mariri (daya daga cikin masu kare lafiyar Limamin na canji) da dai sauransu birjik, Bayan gama addu’ar, wakilinmu ya nemi jin ta bakin wadansu daga cikin manyan masu akidar canji ta Alhaji Muhammadu Abubakar Rimi, irin su Alhaji Dauda Raula da Alhaji Bala Muhammad Gwagwarwa kan matsayinsu gane da siyasar uban-gida da ta cukwikwiye siyasan Nijeriya.
Sun bayyana ra’ayinsu kan siyasar ta uban-gida da kuma hanyar da za a bi a magance ta. A cewar Alhaji Bala Gwagwarwa, babbar matsalar da ta sami jam’iyyu ita ce, a yanzu ba a daukaka manufar jam’iyya a sa ta a gaba a nemi kuri’ar jama’a da wannan manufar, inda ya bayyana cewa, ana daukaka manufar dan takara ta karan kansa, wanda a cewarsa matsala ce babba ga ci gaban siyasar jiha da kasa baki daya.
Da ya juya kan siyasar ubangida kuwa, Gwagwarwa ya ce, “Uban-gida a siyasar Nijeriya wajibi ne, tun lokacin da aka fara siyasa a kasar nan, sai dai a yanzu an yi rashin sa’a cewa, yawancin iyayen gidan da ake yi sai ka dauke shi a matsayin uba shi kuma ya dauke ka a matsayin bawa, sabanin a da wanda abin da uban-gidanka yake kokarin yi shi ne ya dora ka a kan haryar da shi ma ya bi ya yi nasara” Sai dai ya ce, har yanzu akwai hanyar da za a bi a gyara wannan matsalar da ta addabi siyasar kasar kasancewar babu abin da ba zai yuwu a gyara shi ba, musamman idan aka sami shugabanni adalai wadanda ba su da san kansu.
Ya kara da cewa, tsarin da aka dauko yanzu suna nan suna ta kokarin ganin cewa, zaben da zai zo a nan gaba sai an sami shugaban da za a zaba a kan akida ba wai a kan alakarsa da wani babban dan siyasa ba, inda shi kansa shugaban zai ga yadda aka zabe shi bisa akida ta yadda shi kansa zai yi wa jama’a aiki ba tare da lura da cewa, sai ya faranta wa uban gidansa ba.
A nasa bangaren, Alhaji Dauda Raula ya bayyana cewa, “Ni ina daya daga cikin wadanda suke kyamar siyasar uban-gida, a halin yanzu a harkar siyasa ba a neman mu, ba a yi da mu kuma ba a neman shawararmu, san zuciya da rashin adalci shi ya jawo ake irin wadannan abubuwa na rashin kangado a harkar siyasa da jam’iyyu” Daga bisani ya bayyana hanyar da za a bi a gyara, inda ya yi kira ga jama’a da su fito a zabubbuka masu zuwa, su zabi mutane nagari wadanda za su tabbatar masu da ‘yancinsu da kuma yi masu ayyuka nagari.
Ya kara da cewa, tsame su da aka yi daga siyasar jiha gaba daya aka ce sai dai su tafi kananan hukumominsu su yi, shi ya kara hassala matsalar da ake samu a siyasar jihar Kano, inda ya yi nuni da cewa, a da lokacin da suke PRP, shi ne yake kula da kananan hukumomin Gezawa da Minjibir da kuma Dambatta, bisa dukkan wata matsala da za ta taso shi ne zai yi kokarin magance ta sai dai inda ta fi karfinsa ya turo ta zuwa jiha.
A yanzu ba ka da ikon ka je wata karamar hukuma domin domin gyara wani abu da ya shafi siyasa sai a ce kai ba dan karamar hukumar ba ne.
Da aka juwa kan gudummawar da limamin-canji ya bayar wajen ci gaban jihar Kano da al’ummarta, tsohon shugaban karamar hukumar Kabo, Alhaji Salisu Abdullahi Kabo da kuma tsohon dan takarar majarisar tarayya a karamar hukumar Gwale, Alhaji Ibrahim Isa Rabo sun bayyana cewa, tsohon gwamnan na Kano shugaba ne nagari mai kuma sadaukarwa da aiki tukuru, wanda yake jan mutane a jiki da kuma karbar shawarwarinsu a duk lokacin da suka zo da wani abu mai kyau wanda zai bunkasa jihar Kano da kuma kowa wa al’ummar jihar ci gaba.
Sun kara da cewa, ayyukan ci gaba da Alhaji Muhammadu Abubakar Rimi ya kawo wa jihar Kano (Kano da Jigawa) ba zai yiwu ba a iya lissafa su ba, inda suka hada da bangaren ilimi da samar da ruwan famfo a birane da karkara da bangaren kiwon lafiya da ayyukan noma da gine-ginen hanyoyi a birane da karkara da kuma samar da hasken lantarki. Bugu da kari, a cewarsu, Rimi ne a bisa tunaninsa na bunkasa karkara ya zama gwamna na farko a Nijeriya da ya samar da hukuma mai kula da ci gaban karkara mai suna Rural Debelopment Agency da kuma hukumar yada ilimin manya Mass Education wadda ta himmatu domin ilimantar da manya wadanda ba su sami ilimin zamani ba tun daga farko.
A karshe, wakilanmu a wajen taron addu’o’in, Aliyu Umar da Mahmud Gambo Sani, sun yi kira ga kwamitin shirya taron da a ja damara sosai, nan gaba a kyautata tsarin gayyato jama’a domin mahalarta musamman masu akidar ci-gaba su yi cikar kwari.