AFAN, A rubanya kokari wajen bunkasa tattalin arziki – Ganduje

Jihar Kano
Tura wannan Sakon

Daga Mahmud Gambo Sani

Gwamnan jihar Kano Dokta Abdullahi Umar Ganduje ya yi kira ga kungiyar manoma ta kasa (AFAN) da su kara rubanya kokarinsu wajen bunkasa tattalin arziki don ci gaban kasa.

Gwamnan wanda Mataimakinsa Dokta Nasiru Yusuf Gawuna ya wakilta a wajen bude babban taron manoma wanda Kungiyar manoma ta kasa ta shirya a gidan gwamnatin Kano.

Gwamnan yi kira ga manoma da su tabbatar da cewa an ji muryar kungiyarsu a duk fadin kasar nan musamman ta hanyar shirye-shiryensu da nufin inganta ayyukan noma.

Ya kuma bayar da tabbacin cewa gwamnatin jihar Kano za ta ci gaba da hada kai da manoma wajen bunkasa ayyukan noma musamman noman rani, inda ya kara da cewa gwamnatinsa ta bullo da sabbin dabaru don hana asara a bangaren noman.

A nasa jawabin , Ministan noma da raya karkara, Alhaji Sabo Nanono ya bayyana cewa ya zuwa yanzu ma’aikatarsa ​​ta yi rijistar kimanin manoma miliyan shida a duk fadin kasar nan a kokarin da suke na kusanto da manoma ga gwamnati.

Ya kuma yaba wa kungiyar ta AFAN saboda shirya babban Taron, inda ya bukaci shugabannin kungiyar da su rungumi mambobinsu wuri guda, sannan kuma ya yi kira a gare su da su kara shiri kuma su tsaya kan kafafun su.

A nasa jawabin, Shugaban riko na kungiyar, Alhaji Faruk Rabi’u Mudi ya ce sun fara shirin sake fasalin kungiyar ta AFAN tun daga matakin farko har zuwa matakin kasa tare da shigo da kungiyoyin masu kayayyakin amfanin gona cikin tsarin.

Ya kara da cewa shugabancinsa ya raba kayayyakin noma na sama da Naira miliyan 100 ga manoma ta hanyar Ma’aikatar Noma da Raya Karkara.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *