AFCON 2021: Eguaboen ya musanta batun ajiye aiki

Afcon 2021: Eguaboen ya musanta batun ajiye aiki

Eguaboen ya musanta batun ajiye aiki

Tura wannan Sakon

Kociyan rikon kwarya Agustine Eguaboen ya yi watsi da batun cewar ya bar aikin horar da Najeriya, bayan da aka yi waje da tawagar a Afcon.

Super Eagles wadda ta lashe kofin Afirka karo uku, ta yi rashin nasara a hannun Tunisia da ci 1-0 a wasan zagaye na biyu ranar Lahadi a Garoua. Tawagar Najeriya ce kadai ta ci dukkan wasa uku a cikin rukuni, bayan da ta doke Masar da Sudan da kuma Guinea Bissau a rukuni na hudu. Karon farko da Super Eagles ta yi wannan bajintar a gasar cin kofin nahiyar Afirka tun bayan 2006.

‘’Na karbi aikin rikon kwarya, bayan da aka sallami kocin Najeriya, saura wata daya a fara gasar cin kofin nahiyar Afirka. ‘’Ni nake shugabancin sashen masu horar da tamaula a hukumar kwallon kafar kasar, kuma kamar yadda tsarin ya ke, idan aka sallami koci nan take nine ya kamata ya ja ragama kafin a nada wani.

‘’Saboda haka dalilin da ya sa kuka ganni a wannan aikin na rikon kwarya – Wasu ‘yan jarida kan sauya kalamai, wanda hakan bai da ce ba. Amma haka muke ta hakuri. A karshen watan Disamba, Najeriya ta nada Jose Pesseiro, domin maye gurbin Gernot Rohr, inda kocin dan kasar Portugal ya bi Super Eagles Kamaru a matakin mai sa ido.

To sai dai kuma Eguaboen ya ce bai da tabbaci ko zai ja ragamar Super Eagles wasan neman shiga gasar cin kofin duniya da za a fafata gida da waje da Ghana a cikin watan Maris.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *