Aikin Hajjin bana sai godiya -Alhazan Bauchi

Gwamna Bala

Tura wannan Sakon

Godiya ta musamman zuwa ga gwamnanmu, Sanata Bala bisa yadda ya bayar da dama da duk wani tallafi ga Alhazai da za su gudanar aikin Hajji ba tare da matsi ko wani tunani ba ta offishin hukumar jin daddin Alhazai na jihar Bauchi tun daga gida Nijeriya har zuwa kasa mai tsarki.

Jinjina ta musamman ga Amirul Hajj na bana wanda mataimakinsa ya Jagoranta a kasa mai tsarki, Alhaji Abubakar Y. Suleiman (Dan Galadiman Ningi) da ‘yan majalisarsa yadda suka jajirce da sa’ido wajen ganin an gudanar da komai cikin sauki ga Alhazanmu na Jihar Bauchi. Muna kara godiya ga sauran shugabanni wanda suka gabatar da Hhidima ga Alhazan jihar ba dare ba rana, Allah ya saka masu da alheri.

Godiya zuwa gun Malamanmu yadda suka karantar da mu da wa’azantar da mu kullum yadda za mu yi aikin Hajji mai kyau. Godiya ga Alhazan jihar Bauchi yadda suka yi biyayya da da’a ga duk wanda aka nada a matsayin mai yi musu jagoranci kuma suka bishi ba tare da matsala ba.

Alhazan Bauchi mun kara gode wa Allah sannan kuma mun gode wa gwamna, Sanata Bala domin duk wanda ya zo aikin Hajjin shi zai bayar da labarin abin da ya gani da idonsa. Mun tsinci kanmu cikin jin dadi da walwalla da kulawa ta musamman a ko wani lokaci.

Shugabanninmu da Malammanmu da Alhazanmu na Jihar Bauchi dukkansu sun gabatar da addu’o’i neman zaman lafiya ga kasa da kuma jiharmu ta Bauchi, kuma sun yi addu’a Allah ya sa a gudanar da zaben 2023 cikin lafiya, kuma sun yi addu’a ga kawunansu da iyalansu da abokanansu gaba daya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *