Akidar Interfaith: Kura da fatar akuya (I)

Sheikh Muhammad Ibn Usman
Daga Sheikh Muhammad Ibn Usman
Shimfida: Da sunan Allah Mai rahamah Mai jin kai. Tsira da Aminci su kara tabbata ga Manzon Allah, Iyalan gidanshi da kuma dukkanin Sahabbanshi haka ma wadanda suka bisu da kyautatawa har zuwa ranar karshe.
Bayan haka: Wannan ‘yar makala tawa manufarta bayani ne kan: Me a ke nufi da “Interfaith”? Mafarin harkar. Tirka-tirka kan suna/ lakabi Hange da sako (Bision and mission) Karkarewa Kammalawa Me a ke nufi da ‘Interfaith’? Wannan kalma tana da bangarori biyu: ‘Inter’ da kuma ‘Faith’.
Ita kalamar ‘inter’ wadda ta kan zo a matsayin ‘tokarar baya’ wato ‘prefid’ na nufin siffanta wani abu ne tsakanin bangarori guda biyu. Shi ya sa a misali, a ke cewa: ‘International’ wato tsakanin kasa da kasa ko ‘lnter party’ wato tsakanin jam’iyya da jam’iyya da sauransu.
Wato ka ga sabanin cewa ‘intra’ kenan. Wannan kuma ai kaga yana nufin bangare daya ne kawai, abu ne na ckin gida, kamar kace ‘intra party’, wato al’amari da ya shafi cikin gida na wata jam’iyya. Daya bangaren kuma shi ne sunan wato ita kalmar ‘Faith.
Kenan idan a ka ce ‘Interfaith’ to siffantawa a ke nufi. Ma’ana wani al’amari ne TSAKANIN addinai ko kuma akidu. Idan kuma a ka ce ‘Inter party’ a na nufin alaka tsakanin jam’iyyoyi kenan.
Haka dai haka dai… Mafarin harkar: Tun a shekarar 1893 (wato shekaru 129 kenan da suka wuce!), tun daga 11 zuwa 27 ga Satumba na dai ita wannan shekarar 1893 a wani zaure mai suna The Art Institute of Chicago a birnin Chicago da ke Jihar Illinois ta America a ka sa digon lamba na ita wannan harka ta ‘Interfaith’.
Daga cikin fitattun jagororin samar da tafiyar kuwa akwai wani mutum mai suna Charles Carrol Bonney wanda a ka bayyana shi da cewa wani ‘bagidaje’ ne, wato ‘layman’.
Kuma dai shi wannan mutumin – Charles Carrol Bonney- shi ne wanda ya nada Henry Barrows -wani malamin Coci- a matsayin shugaban babban Kwamitin taron na 1893 a Chicago.
Babban darakta na ita wannan tafiya a yanzu shi ne Rabaran ne na Coci! Masana keke da keken abinda ke gudana game da wannan tafiya sun ce wannan taro shi ne na farko kuma jagaba wajen samar da kuma wanzar da ita wannan tafiya ta ‘Interfaith’ a tsare.
To ka ga ashe da lauje cikin nadi, tunda asalin tafiyar ga inda ta fito. Haka yazo a wata makala a kan wannan taro mai kanun: Religion & Ethics Newsweekly, 23 October 2015.
Tsokaci: Yau shekaru dari da ashirin da tara (129) kenan da fara wannan harka ta ‘Interfaith’ a duniya. Abin tambayar a anan shi ne: WANI ZAMAN LAFIYA, TSARO DA KWANCIYAR HANKALI HARKAR INTERFAITH TA KAWO MA MUSULMI A MATAKI NA DUNIYA (GLOBALLY) KO A MATAKI NA YANKIN AFIRKA (CONTINENTALLY) HAKA KUMA A MATAKI NA CIKIN ƘASA (NATIONALLY) KO MA A MATAKI NA TSUKI NA YANKI (LOCALLY)? Wannan tambaya ya kamata a jefo ta saboda masu da’awar wai da ana irin wannan haduwar irin ta gambizar’Interfaith’ wai da an daina samun rigingimu tsakanin Kirista da Musulmi.
Ga adadin shekarun nan, amma har yanzu babu jini mafi arahar zubarwa yau a Duniya irin jinin Musulmi!! Mun tsira a Filasdinu da Kashmir da Irak da Syria da Rohingya a kasar Myanmar?! Mun tsira a yakin basasar tsohuwar Yugoslabia(Bosnia da Herzegobina)?. Su wa a kayi watandar rayuwarsu a Norway 22 ga July 2011 inda ‘yan ta’adda Anders Behring Breibik ya kashe rayuka 77 mafi yawansu Musulmi? Haka kuma menene laifin Musulmi 51 da ‘yan Ta’adda Brenton Tarrant ya kashe ranar 15 ga Maris(March) 2019 a Masallacin An-Noor da ke Christchurch da kuma Linwood Islamic Center dukkaninsu a New Zealand?? Da sauransu da yawa. Haka ma a nan gida Nigeria, su wa ake zalunta yawanci in ba Musulmi ba a fagage da dama?.
(ko da yake sakacinmu yana da muni). Misali kwaya daya: a Jihar Taraba, me ya hana dan ‘Interfaith’ kwato wa musulmi mafiya rinjaye hakkinsu na yin mulkin ita wannan Jihar ta hanyar lumanar tattaunawa domin ai ance”Democracy is a game of Number”?. Ai gashi nan a yanzu haka babu gawamna daya Musulmi a Kudancin Nigeria in banda Gwamna Ishak Gboyega Oyetola na Jihar Osun.
Su wa ke da rinjaye tsakanin Musulmi da Kirista a Lagos, Oyo, da Osun? Abin fahimta dai shi ne Allah(SWT) Ya fada cewa: “Har abada Yahudawa da Nasara ba za su taba yarda da kai ba har sai ka bi hanyarsu (addininsu)” alBakarah:120 Karkashin fahimtar wannan Ayar ashe duk wanda ka ga Yahudu da Nasara da sauran munafukai suna yabonshi akan zakewarsa akan wannan harka ta ‘Interfaith’ ka san ya sauka daga turbar gaskiya.
Abin lura: Zaman tare cikin lumana da jituwa da kuma mutunta juna a kasa irin tamu ta Nigeria ya zama wajibi, tare da tattaunawa akan mas’aloli da suka shafi zamantakewa duk hakan babu laifi (muddin ba’a kaucewa dokokin Allah ba). Hakan kan zo ne domin wanzar da zaman lafiya tsakanin al’umma.
Sai dai ba zai yiwu ba ne a shigo da wani shiri wanda ke dauke da lauje(ko ma barandami) cikin nadi amma a lullube shi da wani kirari ko suna mai jan hankali domin kaiwa ga wata manufa.
Nan gaba kadan bayanin manufar zai bayyana- in shaa Allahu a gabar hange da sako(bision& mission) Tirka tirka kan suna/ lakabi Wasu na kiran harkar da suna ‘Interfaith’ wasu kuma suce/ ‘Inter-religious’, wasu su kuma cewa suke ‘Interbelief’ alhali kuma wasu na ce musu ‘Interpath’. Wato dai kaga a nan sunaye ko ladubba guda hudu kenan amma duk na wani abu guda daya. Kowa yana da mahangar da ya ke kallo wajen zabo wadannan sunaye da ladubba.
Wasu ma sun kara da kiran hadakar a matsayin wai hadakar addinai masu bin akidar Annabi Ibrahim- ‘alayhis Salaamu(Wato the Abrahamic faiths)! Sun samu kansu cikin dawurwura da dimuwa dangane da suna da kuma lakabi. Da farko, mu fara da shi wannan kirari na ‘the Abrahamic faith’ wato WAI gangamin addinai masu bin karantarwar Annabi Ibrahim-’alayhis Salaamu.
Hikimarsu da azancinsu a nan shi ne tunda addinin Musulunci da Kiristanci da kuma Yahudanci dukkaninsu suna da alaka da Annabin Allah Ibrahim ‘alayhis Salaamu ta fuskar salsala da dangantakar jini, to yayi daidai a kira addinansu da wannan lakabi ‘Addinai Ibrahimawa’ wato ‘Abrahimic faiths’.
Allah- ‘Azza wa Jalla- tuni Ya karyata wannan dangantaka muzayyafah. A cikni Suurah ta 3 aayah 67 da kuma ta 68 Ma’ana: