Alhaji Ahmadu Haruna Zago

Alhaji Ahmadu Haruna Zago

Alhaji Ahmadu Haruna Zago

Tura wannan Sakon

Hira ta musamman da Dan, takarar shugabancin jamiyyar APC Na jihar Kano, Alhaji Ahmadu Haruna Zago, mai bai wa gwamnan jihar Kano shawara kan harkokin abinci.

 Albishir: Dalilin shiga takararka na shugabancin jam’iyyar APC a jihar Kano? Danzago: Da farko suna Na Ahmadu Haruna Zago dan jamiyyar APC daga mazabar Gwauron Maje a karamar Hukumar Dambatta a jihar Kano, ita jam’iyya ta kowa da kowa ce, amma babu shakka akwai wadanda suka nemi shugabancin da matakai Na mazaba ko kananan hukumomi, jiha ko na kasa, amma ya danganta da irin yadda zai bayar da gudunmuwar SA, mun zabi matakin jiha domin bada gudunmu wa a samu ci gaba, domin a baya mun bayar da gudunmuwa a jam’iyyu kala-kala tun daga jamiyyar NPN, NRC zuwa GCN, ACP, APP zuwa CRC kuma a karshe zuwa jamiyyar APC.

 To gudunmuwar da muke so mu bayar ya biyo bayan kwarewa da muke da shi a fagen shugabancin da mu’amala da jama’a. Albishir: Wacce gudunmuwa ake ganin jamiyyar APC ta bayar a jihar Kano? Danzago: AI duk Wanda ya ke bin siyasar jihar Kano ya San jamiyyar APC ta samu nasarori masu yawa, kadan ka dauko abubuwa guda uku kadai da jamiyyar APC ta zo da shi kamar AMCO Borrower da babban bakin Kasa CBN suke bayar da bashi ga manoma karkashin gwamnati tarayya da gwamnatin jiha ta Dokta Abdullahi Umar Ganduje suke yi na tallafa wa manoma haka gwamnati Kano ta sanya hannu kan yarjejeniya na karbar kayan amfanin gona da nufin biyan bashin da aka karba, wanda ya karfafa wa manoma kwarin gwiwa, kuma irn gudunmuwar jamiyyar APC ke nan a aikin gona, ba irin gudunmuwar ba da korona ta zo, da Nijeriya sai an yi yunwa, domin gwamnati tarayya to bayar da kashi yasa aka shigo da shinkafa, duk inda kasani ana noman shinkafa yanzu gurin ya bunkasa, na biyu jam’iyyar APC kamar harkar man fetur, ‘yan Nijeriya ba su taba tunanin za su daina kwana a gidajen mai ba Albishir: Ranka ya dade wane shiri aka yin a fuskantar matsalar shugabancin jamiyyar APC sakamakon rabe-raben kai da ke cikin ta?

 Danzago: Gaskiya ne babu shakka akwai kalubale, amma ya danganta da shuguban domin in ka duba shugaba aikinsa ya yi adalci, kuma shugaba aikinsa ya hada kan mutane, amma idan shugaba ya yarda ba zai yi adalci ba, shugaba ya yarda gida gida halak ne, ma’ana shi ne kowa ya yi abin da yake so ya yi abinda ba bu wanda zai ce a bari, wannan akwai matsala, amma mu idan Allah ya yarda, shugabancin da za mu yi shi ne, na hada kan yan jamiyyar APC,ni irin wannan rabe raben kawuna ba zamu yarda da shi ba.

 Albishir : Wace nasara ake ganin an samu a jamiyyar APC a kasa baki daya? Danzago: Idan ka duba jam’iyyar APC a kasa ta na samun gagarumar nasara a duk zabubbukan da ake yi a jihohi, duk da cewa, a wadansu jihohi ba ta samu nasara ba, amma saboda irin yadda jamiyyar ta ke gudanar da shugabanci a tarayya da shgaban kasa Buhari yake yi har wadansu gwamnoni na jam’iyyar adawa ta PDP suna komowa APC, kamar jihar Ebonyi da sauransu jahohi na yankin kudunci, wadanda suna cikin jam’iyyar PDP suka ci zabe amma sun koma jamiyyar APC, amma ba kamar jihar Edo da tun a firamare aka samu matsala rikicin gida inda dan takarar gwamnan jihar ya koma jam’iyyar adawa kuma suka ci zabe, amma duk da haka in ka duba tazarar yawan kuriu. Har yanzu akwai ‘yan jamiyyar PDP masu yawa da suke so su dawo jamiyyar APC a yanzu.

Albishir: Ya za a iya kimanta irin gudunmuwar jamiyyar APC a jihar Kano karkashi jagorancin Dokta Abdullahi Uma Ganduje? Danzago: Na fada maka tun da fari irin gundunmuwa gwamnatin Tarayya da ta jihar Kano, amma a jihar Kano ba shi musaltuwa domin a aikin raya kasa kadai, babu wata jiha a Arewa da za ta yi kafada da kafada da abin da jihar Kano ta yi, idan ka dauki aikin gadojoin nan kadai, kamar na masallacin Dangi na hanyar Zaria Road, dauki hanyar Sabon Gari da ta tashi daga tsohon gidan jaridar Triumph zuwa titin Murtala Muhammad, dubi hanyar da ta tashi daga Bukabu zuwa Kurna har Katsina Road, akwai ayyuka masu yawa ake cikin birni da karkarar jihar Kano da aka yi ayyuka masu tarin yawa wanda duk gwamntin jamiyyar APC karkashin gwamna Dokta Abdullhi Umar Ganduje (Khadimul Islam), ban da maganar gine-ginen makarantu, asibitoci kamar samar da asibitin Giginyu na Muhammadu Buhari da kuma Sheikh Isyaku Rabiu da ke Titin gidan Zoo duk wannan ayyuka wadansu gwamnati ce ta kammala kashi casa’in na aikin, akwai irin wadannan ayyuka da yawa da jamiyyar APC karkashin Alhaji Ahmadu Haruna Zago jagorancin Dokta Abdullahi Umar Ganduje ta yi.

 Albishir: Ranka ya dade ana da labarin Alhaji Ahmadu Haruna Zago da aka fi sani da Danzago a fagen gwagwarmayar siyasa, wai wane ne Dan Zago? Danzago: To ni dai an haife ni a garin Zago a karamar hukumar Danbatta, kuma na yi makarantun Allo kuma na yi gwagwarmaya daban-daban na shiga siyasa a shekara ta1979, a jam’iyyar NPN, ni ne farkon shugaban matasa na jam’iyyar NPN daga 1979 zuwa 1983, sai nan daga 1983 zuwa ‘yan watani hudu, ina cikin mutane 128 wakilan da aka zaba zuwa majalisar wakilai, mu uku ne daga Dambatta, ni ina wakiltar Dambatta East , akwai Dambatta West da Hakimin Makoda yake wakilta, sai Dambatta north da Magaji Tandu ya ke wakilta da Danbatta South da former majority leader, wadannan mutane hudu muka tsaya takara a majalisar wakilai da ni akai wannan zabe na 1983 na 2003, amma jam’iyar PRP suka ci wannan zabe, bayan an gama aka yi jam’iyyar NRC da SDP kuma mun yi kokari mun kawo mazabarmu ta Dambatta, mu ka ci shugabancin karamar hukumar Dambatta, haka kuma na rike campaign director na dan takarar shugaban kasa a NRC da Alhaji Bashir Tofa ya tsaya, sai gwamna, Kabiru Gaya da dan takarar karamar hukumar Dambatta, Kano ta Arewa da ta hada da Dawakin Tofa, Dambatta, Bagwai da sauransu. Ni ne na zama campaign director mai neman kujerarshugaban kasa a wannan lokaci, haka in aka dawo lokacin jam’iyyar DPN da sauransu na shiga jam’iyyar DPN a 1996 a lokacin Marigayi Genaral Sani Abacha, wannan lokaci ni na zama chairman Finance Committee, na jam’iyyar a jhar Kano tare da su Marigayi Musa Gammo, da Sabo Nashe, su Sani Hashim, T. M. Bashir, ni ne shugaban  kwamitin kudi, kuma mun bayar da gudunmuwa kwarai da gaske, sai aka mikawa zaben Dambatta , Kunchi da Makoda kuma na ci zaben, amma a wannan lokaci aka samu canji daga yankin Kura da Garun Malam a lokacin tsohon gwamna Kwankwaso. Sannan aka zo 1993 aka kafa jamiyyar APP, PDP a wannan lokaci Ibrahim Al’amin Little shi ne shugabanta kuma ni ne mataimakinsa, bayan da aka samu matsala aka cire shi aka bani shugabanci, da wannan lokaci aka bani mukami na musamman na mataimaki na musamman kan harkar tsaro a jamiyyar, bayan 1998, kuma ni ne campaign director na Malam Ibrahim Shekarau. Bayan kafa gwamnati na zama mai bai wa gwamna shawara a kan harkokin siyasa watau political matters, akwai kamar su Hamza Darma, bayan jin ra’ayin jama’a sai aka kafa CPC. A lokacin gwamnatin jamiyyar APC karkashin gwamnatin Dokta Abdullahi Umar Ganduje aka bani mai bai wa gwamna shawara a kan harkokin kula da abinci wanda har yanzu nake kai.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *