Al’Mansur ya koka da rashin cika alkawari -Daga wajen gwamnati

Mal. Auwal
Daga Mohammed Ahmed Baba Jos
Shugaban kungiyar ci gaban mazavar Abba na Shehu Malam Auwal Almansur, ya koka da rashin ayyukan ci gaba a mazavar su ta Abba na Shehu da ke garin Jos, ya bayyana irin kalubalen da suke fuskanta shugaban ya bayyanna cewa, akwai wadansu gurare da suka ga an yi masu ayyuka.
Daga cikin kalubalen da suke fuskanta akwai maganar hanya ruwan famfo wutar lantarki da rashin tsaro, ya ce “da farko akwai maganar hanyar New market kasuwar ‘yan tifa wacce tafi tayar masu da hankali, tun da akwai alkawarin da gwamnatin ta yi, na gyaran.
Duk da akwai wadansu hanyoyin da ta yi kamar titin Unguwar Rogo da sauransu, ya ce “mutanen Abba na Shehu suna da korafi, sun yi-sun yi har sun gaji a kan hanyar ta New market, wannan hanya a takaice ta kai kimanin shekaru 3 zuwa 4 da farawa. Tun wa’adin gwamnatin na farko, an kuma kammala wadanda aka fara aikin tare da wannan hanya kuma sun ninka ta a girma.
Ya ce ba za su ce ba su gode ba, tun da an yi wadansu ayyuka kuma a cikin su ne, amma wannan hanya tafi sauran muhimmaci. Saboda hanya ce da take da alaka da tattalin arziki mutanen karamar hukumar Jos ta Arewa da jihar Filato, sannan tana da alaka da lafiyar mutanen kasuwar da mazauna gurin, saboda kura da take damun su, bayan kankare hanyar, ya kara da cewa, da yawa daga cikin mazauna gurin.
Suna fama da tari da Asma duk kurar ta lalata kayan da ake siyarwa a wajen, sannan wadanda suke zuwa siyan kayan wajen sun daina saboda kura sannan lokacin damina ga laka da ake fama da ita, ya ce, ba su ji dadin abin da gwamnati ta yi masu ba. Kullum sai dai a ce za’a yi aikin sannan bai wuce wata uku ba, an sake zuwa da motoci da kayan aiki an zuba kasa an ce za a ci gaba da aikin, ya ce, su shugabanni an mayar da su makaryata a gurin mabiyan su, sun sha cewa, za’a yi aikin yafi sau uku.
Domin haka ya daina cewa, jama’a za’a ci gaba da aikin, sun san an yi wadansu gurare amma hakan ba zai hana su ce ba’a kyauta masu ba, ya ce “ idan kuma ya fadada bayaninsa ga babbar kasuwar Terminus an yi alkawarin za’a gyara lokacin yakin neman zave.
Amma har yanzu ba abin da aka yi, a kan alkawuran da aka yi sun yi wa gwamnati uzuri, duk da babu abin da ya gagari gwamnati, su ba su yi fada da wani ko sun zagi kowa ba, da yake amsa tambaya kan ko za su umarci jama’arsu, su fito zave da za’ayi na kananan hukumomi kasa da wata daya.
Sai ya ce, su ba za su ce kar a fito ba, a kan zargin da aka yi cewa, wadansu ‘yan kasuwa suna kawo cikas kan aikin hanyar ya karyata wannan zargin, ya ce ”idan ma an yi haka to a baya ne amma yanzu idan gwamnati tana so ta yi aiki ta zo taga idan akwai wanda zai hana saboda ya zauna da shugabannin.
Kasuwar da sauran ‘yan kasuwar ya ce “kuma ya fadi matsalar a gidan gwamnati a wani taro da aka gayyace shi a gaban sakateren gwamnatin Pro Danladi Atu, ya kara da cewa” duk Nijeriya babu wanda suke shan wahala kuma ba’ a ba su hakkinsu ba’a daukar ‘ya’yan su aiki sai mutanen Jos ta Arewa.
Daga karshe ya bayyanna cewa, ko ya ya gwara wannan gwamnatin da ta Jonah Jang tun da waccan ba ta ma yarda cewa, Hausawan Jos ‘yan jihar Filato ba ne, ko shin baya ganin wancan gwamnatin ta yi zargin ba su zave ta ba, sai ya ce, sun zavi Sanata da dan majalisa wanda suke cikin gwamnatin.