Ambaliya: Zangon Kabo ya jajanta wa ‘yan-kasuwar Kwari

Ambaliya: Zangon Kabo ya jajanta wa ‘yan-kasuwar Kwari

Ambaliya: -kasuwar Kwari

Tura wannan Sakon

Alhussain daga Kano

Wani dan-kasuwa da ke cikin jihar Kano, Alhaji Mamuda Liman Zangon Kabo, ya nuna alhininsa tare da jajanta wa ‘yan-kasuwar kantin Kwari da ke Kano, a kan ambaliya da suka gamu da ita kawankin baya wanda ya jawo masu asarar miliyoyin Nairori.

Alhaji Mumuda Liman Zangon Kano, ya yi addu’ar Allah ya mayar masu da mafificin alheri ya kiyaye sake aukuwar irin haka nan gaba. Ya kuma gode wa al’ummar da suka taimaka masu musamman masu hali yana fatan mawadatan za su ci gaba da taimaka masu, har ila yau ya kuma tausayawa ‘yan-kasuwar Beirut da suma suka gamu da ibtila’in rugujewar gini.

Dan kasuwar ya yi amfani da wannan dama da jinjina wa gwamnan jihar Kano, a kan umurnin da ya bayar na rushe duk wani gini ko shago da aka gina a kan hanyoyin ruwa musamman wadanda ke kwaryar Ambaliya: Zangon Kabo ya jajanta wa ‘yan-kasuwar Kwari birbin jihar, yawancin ambaliyar da ake samu yana da danganta taka da toshe magudanan ruwa ko kuma rashin yashe magudanan ruwan.

Har ila yau, ya kuma roki gwamnan da ya gyara hanyoyin cikin garin nan domin duk wandanda suke bin hanyoyin sun san suna bukatar kulawar gwamnatin jihar. Daga karshe, ya yi addu’ar Allah ya kara bai wa jihar Kano da kasar nan zaman lafiya da kwanciyar hankali ya kawo mana karshen garkuwa da ake yi da mutane domin karbar kudin fansa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *