An gano dabarun noman dawa -Abdullahi Ali

Noman Dawa
Shugaban qungiyar masu noman dawa a jihar Kano, Alhaji Abdullahi Ali Maibiredi, wanda kuma shi n e shugaban hadaddiyar qungiyar manoma ta qasa reshen jihar Kano (AFAN) ya bayyana cewa, a yanzu manoma sun sake farkawa kan noman dawa domin amfanin al’umma, kasancewar an gano ana yin abubuwa da yawa da ita, wadanda suka hadar da magunguna na magance cututtuka masu yawa.
Alhaji Abdullahi Ali ya bayyana hakan ne lokacin da yake ganawa da manema labarai a gidan gwamnatin jihar Kano lokacin da ake tsaka da gudanar da taro kan noman dawa, ya kuma qara da cewa, a yayin bitar an sanar da su abubuwa muhimmai da za su ba su damar ci gaba da qwarewa cikin samun albarkar noman dawar.
Haka kuma ya ce, a baya dawa kala hudu kawai aka sani amma yanzu an gano kalolin ta 69,a dangane da haka ne ya qalubalaci manoman dawa da su tabbata sun rungumi sababbin dabaru domin cim ma nasarorin da a ka sa gaba.
Da ya koma ta kan gwamnatocin jihohi da ta tarayy akuwa buqatarsu ya yi da su samar da duk irin tallafin da ya kamata ga manoman dawa domin ci gaba da habaka noman dawa a Nijeriya.