An samu raguwar hadura a Kano -Kwamanda Zubairu Mato

Kwamanda Zubairu Mato

Tura wannan Sakon

An bayyana raguwar hadura a hanyoyin da sukai hadaka da jihar Kano a cikin lokacin da muke ciki. Hakan na fitowa ne daga bakin Sakta Kwamanda Zubairu Mato a wata zantawa da manema labarai ranar Litinin a ofishinsa na jihar Kano.

Kwamandan ya ce, hukumar kiyaye hadura ta kasa reshen jihar Kano tana aiki ba dare ba rana wajen aiki dmin kara sa’ido tare da kare a kaf titunan da ke jihar.

Mato ya kara da cewa, kasancewar jihar Kano cibiyar kasuwanci ce tare da yawan al’umma da ke shige da fice da ya sa hukumar ta bullo da hanyar sintiri da sa’ido a koda yaushe kan to titunan da suka hada jihar Kano da sauran jihohin Kaduna da Katsina da Jigawa wanda hakan ya haifar da da mai ido wajen rage afkuwar hadura.

Ya ce, koda yaushe suna tura kwararrun jami’ansu zuwa cibiyoyin addinai da tashoshin mota da sauran gurare domin taron wayar wa da al’umma kai domin magance tukin ganganci da gudun wuce sa’a da yake haifar da hadari da salwantar rayukan wanda ba su ji ba ba su gani ba.

Kazalika ya bayyana cewa, babban kalubalen da suke fuskanta koda yaushe shi ne, mafi yawancin direbobi ba sa bin dokokin tuki da ake gindaya masu. Ya kuma bukaci direbobi da sauran masu amfani da ababen hawa da su guji tukin ganganci domin kiyayewa da kawo karshen salwantar rayuka kan hanyoyi da duk inda suke.

Daga karshe, Zubairu Mato ya ce, a shekarar da ta gabata an samu hadura guda 255, wanda rayuka 85 suke salwanta yayin da mutane 1036 suka jikkata da raunuka.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *