An yi wa gwannan Zamfara riga-kafin korona

An yi wa gwannan Zamfara riga-kafin korona
Daga Shu’aibu Ibrahim Gusau
A yau ne aka kaddamar da alluran rigakafin korona wanda gwamnan jihar Zamfara, Alhaji Bello Muhammad ya karbi alluran rigakafin a matsayin wanda aka fara da shi, an kaddamar da allurar ne a fadar gwamnatin jihar dake Gusau.
Bayan kammala yi masa allurar Matawallen maradun ya bukaci duk dan jihar Zamfara da ya aminta a yi masa allurar ta rigakafi, ya ce, rigakafi ne ga annobar da ake fama da shi a wannan kasa ta mu.
Ya kuma ce, za’a ci gaba da wannan allura zuwa ma’aikatun gwamnati , ya ce, duk wanda ya ke so za’a yi masa, ya ce, kyauta ake yi ba’a biyan ko sisi
Shi ma a ci gaba da gudanar da allurar, Kwamishinan ‘yan sanda na jihar Zamfara Mista Abutu Yaro, a ranar Talata, shi ma ya karbi kashi na farko na maganin korona.
Muhammad Sa’idu na asibitin ‘yansanda na Gusau ne ya ba shugaban ‘yan sanda rigakafin, bayan
kammala wa shugaban ‘yansanda sauran manyan jami’an ‘yan sanda a jihar sun karbi allurar rigakafin a hedkwatar‘ yan sandan da ke Gusau.
Kwamishinan ya bukaci jami’an ‘yan sanda a jihar da su bayar da kansu domin yin rigakafin, ya ce “Ina so in yi amfani da wannan damar in yi kira ga dukkan jami’an‘ yan sanda a jihar da su ba mu hadin kai a wannan aikin.
Alurar rigakafin ba ta da ciwo, ba ta da illa kuma tana da kyau a cikin jiki, domin yana amfani ga lafiyar dan’adam, “A matsayinmu na jami’an tsaro, sai muna da koshin lafiya, za mu iya bayar da gudummawa ga tsaron kasarmu.
“An umarci dukkan ‘yan sanda maza da mata a jihar da su yi rajista kuma su tabbatar sun yi rigakafin.”