Ana yi wa rayuwata barazana – Shugaban EFCC

Ana yi wa rayuwata barazana - Shugaban EFCC

Ana yi wa rayuwata barazana - Shugaban EFCC

Tura wannan Sakon

Shugaban Hukumar EFCC  mai  yaki da cin hanci da rashawa a Nijeriya, Abdurashid Bawa, ya yi zargin cewa, yana fuskantar barazanar hallaka shi daga wadansu ‘yan kasar.

Zargin ya nuna yadda yaki da cin  hancin da rashawa a Nijeriya ke da wahala kamar yadda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya fadi a kwanan nan, a lokacin da yake amsa tambayoyin manema labarai.

Bawa wanda ya sha alwashin sa

mun nasarar yaki da cin hanci da rashawar da ya saka a gaba, ya ce, a ‘yan kwanakin da suka gabata ya samu barazana daga wani mutuum wanda Hukumar EFCC ba ta gudanar da bincike a kansa.

Shugaban hukumar ya ce, ya karbi wayar wani babban mutuum lokacin da ya ziyarci birnin New York inda mutumin ya shaida masa cewar zai kashe shugaban EFCC, dan yaron nan’.

Ya ce, wannan na daga cikin abin da ke nuna yadda mutanen da suka saci dukiyar talakawa ke yaki da ayyukan da hukumar ke yi, yayin da yake cewar yana da yakinin za su samu nasara a kai.

Shugaban na EFCC ya kuma ce, suna sanya ido a kan mutanen da ke halatta kudaden haramun daga bangaren ma’aikatan gwamnati da kuma masu zaman kansu a yunkurin da suke yi na dakile matsalar da ke bata wa Nijeriya suna.

Daga cikin hanyoyin da Bawa ya ce, suke dauka, har da amfani da shugabannin addini wajen ci gaba da fadakarwa dangane da illar cin hanci da rashawa a tsakanin al’umma.

A watan Fabarairun da ya gabata, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada Abdurashid Bawa a matsayin sabon shugaban Hukumar EFCC domin maye gurbin Ibrahim Magu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *