APC, a tabbatar wa Acida shugabancin jam’iyya

apc

Alamar APC

Tura wannan Sakon

Musa Lemu Daga Sakkwato

Shugabannin jam’iyyar APC na Kananan hukumomi 23 da ke jihar Sakkwato sun yi kira da uwar jam’iyya ta Kasa da ta tabbatarwa, Alhaji Isa Sadik Acida shugabancin jam’iyyar a jihar.

Da yake jawabi ga taron manema labarai a ranar Asabar da ta gabata a Sakkwato a madadin shugabannin jam’iyyar APC na Kananan hukumomi 23 da ke jihar, Alhaji Muhammadu Musa Sarkin Alaru ya ce, shugabannin Kananan hukumomi 23 su ne suka haDu suka zaBi Alhaji Isa Sadik Acida a matsayin shugaban jam’iyyar APC a jihar Sakkwato a yayin da aka Kaddamar da taron jam’iyya a babban ofishin jam’iyyar da ke Sakkwato.

Ya ce, ganin yadda suka kasance halaltattu ya sanya kwamitin rikon Kwarya da uwar jam’iyyar ta Kasa ta kafa suka Kaddamar da shugabannin a babban ofishinta da ke Sakkwato bayan amincewa da sahihin zaBe da ya gudana da aka gudanar a ranar 8 ga watan Nuwamba 2021 a inda aka zaBi Isa Sadik Acida a matsayin shugaban jam’iyya na jihar Sakkwato.

Hakazalika shugabannin suka tabbatar cewa, tsohon gwamnan jihar Sakkwato Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko shine babban jagoran jam iyyar APC a jihar JARUMI UBAN TAFIYA.

Anan sai suka yi kira ga Ministan Shari’a Abubakar Malami da ya kama kansa ya kuma kama bakinsa kazalika ya koma jiharsa na haihuwa watau jihar Kebbi domin ya gyara zamansa da al’ummar jihar kan ire iran katobaran da ya aikata a jihar Kebbi.

A saboda haka suka gargadeshi daya daina yin katsalandan a kan harkokin wasu jihohi tare da yin soki burutsu ya kuma sani cewa, jihar Sakkwato ba kanwar lasa ba ce.

Alhaji Muhammad Musa sarkin Alaru ya ce, zaBensu da aka yi a KarKashin jam’iyyar APC a jihar a ranar 4 ga watan Satumba 2021 shi ne sahihin zaBe na halaliya da babu maguDi ko kuma taKaddamar zaBen ya kasance cikin nasara da ya sami jinjina daga shugabannin kwamitin riKo na Kasa.

Daga Karshe, shugabannin a KarKashin jagoransu, Alhaji Muhammadu Musa Karkin Alaru suka yi kira ga shugaban jam’iyyar na Kasa mai adalci Mai Mala Buni da ya tabbatar wa Alhaji Isa Sadik Acida shugabancin jam’iyyar ganin cewa, shi ne halatccan zaBaBBen shugaba

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *