APC da PDP duk kanwar ja ce-’Yan Nijeriya

APC da PDP duk kanwar ja ce-’Yan Nijeriya

APC da PDP duk kanwar ja ce-’Yan Nijeriya

Tura wannan Sakon

Manyan jam’iyyun siyasar Nijeriya guda biyu APC da PDP sun kasance daya daga cikin batutuwan da ‘yan kasar ke tattaunawa a shafukan sada zumunta.

Wannan na zuwa sakamakon sauya sheka da tsohon ministan sufurin jiragen sama Femi Fani-Kayode ya yi daga PDP zuwa jam’iyyar APC, wanda ya yi kaurin suna wajen caccakar gwamnatin APC ta shugaba Buhari.

Haka kuma batun ya kara jan hankali sakamakon rahotannin da ke cewa Sanata Shehu Sani ya sauya sheka zuwa jam’iyyar PDP daga PRP, wanda daga APC ya koma PRP.

Mista Femi Fani-Kayode, a ranar Alhamis ya ce ya yi kuskure game da sukar da ya yi wa gwamnatin Muhammadu Buhari a baya.

A wata hira da kafar Channels, FaniKayode ya danganta abubuwan da ya aikata a baya da cewa “saboda rashin sanin Shugaba Muhammadu Buhari sosai a lokacin.

” Yadda APC ta karbi Fani-Kayode ne ya ja hankalin ‘yan Najeriya inda suke bayyana cewa babu ba ta da bambanci da PDP.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *