APC tana neman mai ceto -Nabature

Alamar APC
Daga Shu’aibu Ibrahim Gusau
Wata kungiyar masu kishin kasa reshen jihar Zamfara, ta roki shugaban kasa Muhammadu Buhari da dattawan jam’iyyar APC da su ceto jam’iyyar daga hannun wadansu da ke neman wargaza jam’iyyar.
Shugaban kungiyar, Alhaji Ibrahim Nabature ne ya yi kiran lokacin da yake zantawa da manema labarai a Gusau jihar Zamfara.
A cewarsa “Akwai wadansu da ke kokarin ruguza jam’iyyar kafin zaben 2023 idan har abubuwa ba su tafi yadda suke so ba,” in ji Nabature.
Shugaban ya ce, kungiyar ta lura da yadda wadansu gwamnonin suke kokarin durkushewa suna kuma kokarin ruguza jam’iyyar.
Kungiyar ta yi nuni da cewa, idan har ba a yi la’akari da wuce gona da iri na gwamnonin APC ba, jam’iyyar za ta zama tarihi kafin zaben 2023.
Nabature ya bayar da misali da rikicin da ya dabaibaye jam’iyyar a jihohi da dama sakamakon tarurrukan da jam’iyyar ta gudanar a baya-bayan nan a matsayin yunkurin da wadansu gwamnonin jam’iyyar suka yi da gangan na lalata jam’iyyar da suka yi amfani da su a matsayin dandalin zabe.
Shugaban kungiyar ya roki shugaban kasa da dattawan jam’iyyar da su sa baki domin ceto jam’iyyar. Ya kuma yi watsi da rade-radin da ake yadawa na cewa, tsohon gwamnan Zamfara, Abdulaziz Yari Abubakar, dan takarar shugabancin jam’iyyar APC na kasa ya koma jam’iyyar PDP.
Ya ce “Alhaji Abdulaziz Yari, dan gidauniyar APC, bai taba tattaunawa ko tunanin barin jam’iyyar ba tare da sanin hakikanin magoya bayansa a fadin kasar nan ba,” in ji shi.