Asibitin Aminu Kano zai horar da dalibai 60– masu digiri-digiri kan dakin gwaje-gwaje

Asibitin Aminu Kano zai horar da dalibai 60

Asibitin Aminu Kano zai horar da dalibai 60

Tura wannan Sakon

Daga Aliyu Umar

Dalibai masu digiri-digiri kan kimiyyar dakin gwaje-gwajen cututtuja daga jami’o’in ketare daban-daban,za su sami horo na tsawon shekara daya a asibitin koyarwa na Malam Aminu Kano,da ke Kano.

Da yake gabatar da jawabi wajen bude taron,Larabar da ta gabata, shugaban asibitin, Farfesa Abdul-Rahman Abba Sheshe, ya hore su da su zamo jakadu nagari a asbitin,masu aiki tukuru kuma masu sani ya-kanata,a yayin daukar horon.

Takardar bayani da ke dauke da sanya hannun mataimakiyar daraktar yada labarai da hulda da jama’a ta asibitin,Hajiya Hauwa Muhammad Abdullahi,ta ce, a matsayinsu na jami’an kiwon lafiya,ya kamata su bayar da hidima abin misali wajen yaki da annobar korona kuma su karfafa gwiwar jama’ar gari kan su bi sahu.

A wani bangare na sanin makama,shugaban kungiyar masu kula da dakunan gwaje-gwaje na jihar Kano, Kwamared Shehu Musa,ya yi magana kan nuna kwarewa da kudurorin dakin gwaje-gwaje, kamar kiyaye sirrin majiyyaci da sirrin wanda ya dauke ka aiki da nagartar aiki da aike tare da juna duk da zummar karfafa sha’anin kula da majiyyata da adalci da daidaito. Daliban su fito daga jami’o’i daban-daban har guda 15.

Wadanda suka tofa albarkacin bakinsu a wajen,sun hada da jami’in kula da horon, Surajo Alkassim Muhammad da mataimakin darakta bangaren kula da sinadaren kimiyya a asibitin,da shugaban bangaren kula da dakunan gwaje-gwaje a Jami’ar Bayero,Kano, Dokta Jamilu A Bala da kuma mataimakin shugaban kwamitin bayar da shawara,Dokta Abdullahi Kabir Sulaiman.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *