Asibitin Aminu zai sami na,urar duba masu ciwon zuciya- Sarkin Bichi

Sarkin Bichi ya karbi bakoncin shugabanin asibitin Aminu Kano
Aliyu Umar
Mai Martaba Sarkin Bichi, Alhaji Nasiru Ado Bayero, ya yi alkawarin taimaka wa asibitin koyarwa na Malam Aminu Kano da na,urar duba masu fama da ciwon zuciya.
Ya yi alkawarin ne a lokacin da ya karbi bakuncin kwamitin gudanarwa na asibitin tare da shugabannin gidauniuar Sahara mai agaza wa masu fama da cutar da ke addabar zuciya wadanda suka kai masa ziyarar alfarma a fadarsa da ke Bichi,a jiya Alhamis.
Wata takardar bayani da ke dauke da sanya hannun mataimakiyar daraktan yada labarai da hulda da jama,a ta asibitin,Hajiya Hauwa Muhammad Abdullahi,takce, Sarkin ya ce, yana sane da halin damuwa da masu fama da ciwon zuciyar suke ciki na neman waraka gida da waje.
Mai Martabar ya nuna matukar damuwa kan yadda masu fama da cutar zuciya ke yin wadari tsakanin Abuja da Ikko domin neman magani,inda ya yi kira ga kungiyoyi da daidaikun mutàne masu jinkai da su agaza wa asibitin kuma ya bayar da tabbacin cewa, masaraurar Bichi za ta taimaka wa asibitin a wani bangare na hidimta wa jama,a.
Tun da farko, babban daraktan asibitin, Farfesa Abdulrahman Abba Sheshe shi da tawagarsa sun zo fadar Bichi ne domin yin mubaya,a ga Sarki tare da mika kokon bara gare shi kan kalubalen da asibitin ke fuskanta, musamman rashin na,urar kula da masu fama da ciwon zuciya da katafaren dakin karbar ,yan hadari da masu bukatar kulawar gaggawa