Asibitin koyarwa na Aminu Kano ya yi allurar Korona- Shugabanni na sahun gaba

A yau mukaddashin babban daraktan asibitin koyarwa na Aminu Kano, Farfesa Auwalu Umar Gajida,ya jagoranci yi wa shugabannin allurar riga-kafin korona.
Da yake gabatar da jawabi jim kadan da yi masa tasa allurar,mukaddashin daraktan asibitin koyarwa na Aminu Kano, ya ce, tuni aka ware wajen ci gaba da aikin gobe,Jumma’a, cikin yanayi na walwala da ‘yanci.
Daga cikin shugabannin da aka yi wa riga-kafin,akwai mataimakin shugaban Jami’ar Bayero, Farfesa Sagir Adamu Abbas, da Na’ibiñ shugaban Jami’ar Bayero mai kula da bagaren karatu Fatfesa Mahmoud Sani, da Farfesa Gumel,da shugaban kwamitin bayar da shawara kan magunguna na asibitin, Dokta Abdullahi Kabir Sulaimanda Dokta Garba Ibrahim Diggol,da Farfesa Nashabaru, shugaban SERVICOM reshen asibitin, da Dokta Dalhatu Gwarzo,malamin Jami’a,da Malama Zahara’u ta bangaren kula da kiwon lafiyar al’umma,da Sa’idu Shehu Muhammad daga bangaren yada labarai da hulda da jama’a.
Sanarwa dauke da sanya hannun mataimakiyar daraktar yada labarai da hulda da jama’a ta asibitin, Hajiya Hauwa Muhammad Abdullahi.