Askarawan Nijeriya sun fatattaki ‘yan ISWAP, Boko Haram -A Borno

Tura wannan Sakon

A wani harin da sojojin Nijeriya suka kai kan ‘yan ta’addan kungiyar ISWAP da dakarun kungiyar OPHK sun yi raga-raga da su yadda suka kashe da dama daga cikinsu, yayin da suka jefa bama-bamai a sansanin ‘yan ta’addar da ke yankin karamar hukumar Damboa ta jihar Borno.

A wani rahoton da aka tattaro na nuna cewa, an kai wasu hare-hare ta sama da dama daga rundunar sojin saman Operation Hadin Kai a ranar 27 ga watan Nuwamba, 2022, yayin da aka kai hari kan ayarin motocin ‘yan ta’addan a wani wuri da ake ce da shi Kau-Shoro’a. Wata majiyar tsaro daga rundunar sojin sama, ta shaidawa Zagazola Makama, wani kwararre kan yaki da tada kayar baya kuma mai sharhi kan harkokin tsaro a tafkin Chadi cewa, farmakin da jirgin yakin Super Tucano na jirgin yakin Super Tucano ya kai ya yi nasarar yin kaca-kaca da wata mota kirar hilud da ke dauke da wasu mayakan, inda suka kashe dukkan mutanen dake cikinta.

Zagazola ya fahimci cewa gawarwakin ‘yan ta’addar sun bazu ko’ina a wurin yayin da ‘yan ta’addan da suka tsira suka yi ta rantawa a na kare son tsira da ran su.

Majiyar ta ci gaba da cewar, dakarun rundunar sojojin saman Najeriya da ke aiki tare da sojojin sama, za su ci gaba da kai farmakin da suke kai wa a kan ‘yan ta’addan a yankin Arewa maso Gabas.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *