ASUSS ta jaddada kudirin ingata rayuwar ‘ya’yanta

Daga Ahmad S. Ahmad
Shugaban kungiyar Malaman Makarantun sakandare ta kasa reshen jihar Kano ”ASUSS” Kwamared Abdu Usman Yalo ya sake jaddada kudirinsa na ci gaba da habbaka rayuwar mambobinsa, domin samun walwalar aikin koyo da koyar wa ako da yaushe.
Abdu Usman Yaloya bayyana hakan ne ga manema labarai a babban birnin jihar Kano, wanda ya kara da cewa, an kafa kungiyar ne domin samar da warware duka matsalolin da suka damu harkar koyo da koyarwa ga malamai.
Haka kuma ya kara da cewa, tun da yahau kan kujerar shugabancin kungiyar ya samar da nasarori masu yawa,a inda ya kuma ce babbar matsalar da take addabar su a yanzu bai wuce rashin muhalli na kansu ba,wanda a yanzu na haya suke ciki.
A dangane da hakan ne ya nemi masu hannu da shuni kan su tallafa musu kan yunkurin sun a samun tabbataccen muhalin.
Da ya koma ta kan malaman makarantu kuwa Kwamared Abdu Usman Yalo ya neme su da su tabbata sun ci gaba da kulawa kan ayyukansu, tare da rike amanar da aka dora masu.
Daga karshe, ya gode wa gwamnan jihar Kano, Dokta Abdullahi Umar Ganduje kan irin gudummuwar da yake ba su tsawon lokaci, ya kuma nemi da ya taimaka masu da fili domin samar da sakateriyar kungiyar.