Saboda hauhawar farashin kayan masarufi -Gidajen abinci sun yi karin farashi -In ji Abubakar
Daga Musa Diso Manajan gidan abincin Shab`an da ke kan titin gidan Zoo, Malam Yahaya Abubakar ya bayyana hauhawar kayan masarufi musamman kayan abinci da cewa, wani babban kalubale ga ‘yan Nijeriya da ke fuskanta a wannan lokaci na rashin tabbas. Manajan ya yi furucin ne ga wakilin jaridar Albishir a babban birnin Kano makon […]
Neman goyon baya: Osinbanjo ya ziyarci Zamfara
Mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo, jigo a jam’iyyar APC kuma mai neman tsayawa takarar shugaban kasa a zaben 2023, ya ziyarci jihar Zamfara domin ganawar sirri da wakilan jam’iyyar APC a jihar Zamfara. Mataimakin shugaban kasar wanda ya amsa tambayoyin manema labarai jim kadan bayan kammala taron, ya ce, ya gudanar da shawarwari mai inganci […]
A kafa Kwamitin Sasantawa – Domin ci gaban APC a Kano -Usman Dangwari
Daga Jabiru Hassan Shugaban Kwamitin riko na kungiyar masu sana’ar kayan gwari, Alhaji Usman B. Dan gwari ya ce, idan aka kafa kwamitin sasantawa ko shakka babu jam’iyyar APC za ta sami masalaha da daidaito a jihar Kano da kuma kasa baki daya. Ya yi tsokacin ne a zantawarsu da manema labarai a Zariya, inda […]
A Kano: ADC ta bai wa Khalil takara
Daga Mahmud Gambo Sani Fitaccen malamin addinin Misulincin nan, Malam Ibrahim Khalil ya zama dan takarar gwamnan Kano a karkashin jam’iyyar ADC, babu hamayya. Malam Ibrahim Khalil, wanda ya sami takarar a yayin taron kaddamar da takarar tasa da kuma mika masa fom takarar, wanda aka gudanar a ranar Lahadin da ta gabata, a gidan […]
Kashe Deborah ba daukar doka a hannu ba-Sherif Auwal Siddi
Danjuma Labiru Bolari Daga Gombe Alhaji Auwalu Saddik Bolari, daya daga cikin tsofaffin mawakan yabon Manzon Allah, a Gombe, yanzu haka shi ne shugaban kungiyar Ushakun Nabiyi ta kasa, ya bayyana rashin jin dadinsa kan yadda wadansu malamai suke ganin kashe Deborah wadda ta yi batanci ga Manzon Allah da cewa, daukar doka ne a […]
Albishir epaper 20 ga Mayu 2022
Domin samun jaridar Albishir ta 20 ga Mayu 2022 a dunkule danna nan!
Matasa, a guje wa shiga bangar siyasa -Sharif Sidi
Danjuma Labiru, Daga Gombe Yayin da babban zaben shekarar 2023 ke kara karatowa, shugaban majalisar mawakan kasidun Hausa ta Nijeriya watau, Ushakun Nabiyyi Rasulil A’azam, Shariff Auwal Siddi Bolari, ya yi kira ga matasa a Jihar Gombe da Nijeriya su guji duk wani abu da zai iya kawo tsaiko ga zaman lafiya da tsaro a […]
Adalci, dalilin tururuwa zuwa NNPP -In ji Danpass
Daga Musa Diso Wani fitaccen dankasuwa kuma jagora a tafiyar jam’iyar NNPP, Alhaji Muhammdu Gambo Danpass kuma Dan Saran Kano ya ce, adalci ne ya sanya jama’a suke tururuwa zuwa NNPP mai kayan marmari in ji Danpass. Ya bayyana hakan a lokacin da yake zantawa da wakilin jaridar Albishir makon da ya gabata ya ce, […]
Bauchi ta inganta rayuwar jama’arta -In ji Baba Tela
Jamilu Barau daga Bauchi Gwamna Bala Mohammed Abdulkadir na jihar Bauchi ne ya bayyana haka a lokacin da ya karbi bakuncin tawagar cibiyar nazarin dabarun siyasa ta kasa reshen jihar Filato a wata ziyarar ban girma da suka kai ranar Litinin a ofishinsa. Gwamnan jihar Bauchi wanda mataimakinsa, Sanata Baba Tela ya wakilta ya shaidawa […]
Sarkin Kano ya sami lamba mafi daukaka a Senegal
Daga Mahmud Gambo Sani A ranar Litinin da ta gabata, shugaban kasar Senegal, Mista Macky Sall ya karrama Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero da lambar girma mafi daukaka a kasar Bikin wanda aka gudana a fadar gwamnatin kasar, ya sami halartar mukarraban gwamnati da ‘yan tawagar sarki. A jawabinsa na karbar lambar […]