Ayyukan ci gaba: El-Rufa’i ya cancanci yabo -Aliyu Sa’idu

Ayyukan ci gaba: El-Rufa’i ya cancanci yabo
Tura wannan Sakon

Daga Isa Abdullahi daga Zariya

An bayyana ayyukan ci gaba da gwamnan jihar Kaduna Malam Nasiru Ahmed El-rufa’i musamman a kananan hukumomin Sabon gari da Zariya da cewar zai bar tarihin da za a dade ana tunawa da shi shekaru ma su yawan gaske a daukacin jihar Kaduna baki daya.

Wani jigo a Jam’iyyar APC a karamar  hukumar Zariya mai suna Alhaji Aliyu Sa’idu ya yi wannan yabo ,a lokacin da ya yi tsokaci kan ayyukan ci gaban al’umma da gwamna Malam El-rufa’i ya aiwatar da al’ummomin jihar Kaduna za su dade su na mora.

Alhaji Aliyu ya ci gaba da cewar, shekaru da yawan gaske da sika gabata,al’ummar jihar Kaduna ke bukatar wadannan ayyuka daga gwamnatocin da suka gabata,a cewarsa,sai alkawurran za a yi ayyukan gwamninin suka yi, har suka bar mulkin jihar Kaduna ba su cika alkawurran ayyukan ci gaba da suka yi wa al’ummar jihar ba.

Alhaji  Aliyu ya bayar da misali da sabbin hanyoyin da gwamnatin jihar Kaduna ta yi su a birnin Zariya da suka  hada da wadda ta tashi daga kasuwar birnin Zariya zuwa Kofar Galadima da wadda ta tashi daga Kwanar matasa a Unguwar Lalli zuwa Kofar Doka da wadda ta tashi daga Kofar Jatau zuwa Ofishin ‘yan ‘yan Sanda na birnin Zariya.

Sauran ayyukan sabbin hanyoyi da gwamnatin jihar Kaduna ta yi  a karamar hukumar Sabon garin Zariya musamman a Unguwar Turawa (GRA) su na da yawan gaske,da duk Wanda ya san wadannan hanyoyi kafin Malam Nasir El-Rufa’i ya zama gwamnan jihar Kaduna,dole al’umma ke binsu,saboda kammala lalacewa.

A dai zantawar da wakilinmu ya yi da Alhaji Aliyu Sa’idu ya yaba wa gwamnan na gyaran makarantun firamare da kuma sakandare da kuma asibitoci kanana da suke gundumomin knsiloli 255 a kananan hukumomin jihar Kaduna 23,wadannan ayyuka,a cewarsa, a bayyane su ke a wuraren da aka yi su.

A game da shirye – shiryen zaben shekara ta 2023, Alhaji Aliyu Sa’idu ya daga kara ga shugabannin jam’iyyar APC na jihar Kaduna,na laifuffukan da suka yi wa ‘yan siyasa a karamar hukumar Zariya da sauran kananan hukumomi da suke jihar Kaduna.

Wadannan matsaloli da suka faru da duk wani can siyasa a jihar Kaduna ya san wadannan laifuffuka,in an same yin gyaran shi ne zai iya zama matakin farko, a cewarsa, na samun nasarar zabubbukan shekara ta 2023 a karamar hukumar Zariya da kuma jihar Kaduna.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *