Ayyukan raya kasa a Sakkwato: ‘Yan-jarida sun yi rangadin gani-da-ido

Tura wannan Sakon

Musa Lemu Daga Sakkwato

Gwamnatin jihar Sakkwato ta gudanar da ayyuka daban-daban a dukkanin mazabu da ke kananan hukumomi 23 da ke jihar, bisa kudirin gwamnatin na raya karkara domin ci gaban al’ummarta.

A yayin da kungiyar ’yan jarida a jihar ke rangadin gani da ido na ayyukan da gwamnatin ta gudanar a kananan hukumomin Bodinga da Yabo da Shagari da Tambuwal da kuma garin Kebbe, gwamnati ta gyara gidajen iyayen kasa da samar da ruwan sha da gyaregyaren asibitoci da inganta su.

A sama da shekaru 7 da gwamnatin Aminu Waziri Tambuwal ta yi bisa karagar mulki, ta gudanar da gyare-gyaren makarantu da masallatai da gina tankunan ruwa mai daukar fiye da lita miliyon daya domin samar da wadataccen ruwa ga al’umma.

Gwamnatin tana gudanar da ayyukanta ne tare da hadin gwiwar ma’aikatar kula da kananan hukumomi domin cim ma nasarar samun romon dimukuradiyya ga al’ummar karkara.

Gwamnatin ta gina tankin samar da ruwa mai daukar fiye da lita miliyon daya a garin Goronyo tare da gina madatsar ruwa da ke da tsawon kilo mita 7, wadda karamar hukumar ta gina a kan kudi Naira miliyon 35 domin hana ambaliya a tsakanin gidaje da gonaki.

A yayin da yake zagayawa da manema labarai lungu da sako, domin gani da ido dangane da ayyukan da gwamnatin ta gudanar, tare da hadin gwiwar ma’aikatar kula da kananan hukumomi, shugaban karamar hukumar Goronyo, Alhaji Abdulwahab Yahaya Goronyo ya ce, an gina ajujuwan karatu guda 2 a kan kudi Naira miliyon takwas da dubu dari shida, an kuma gina makarantar Islamiyya, wadda aka lakaba wa suna da Nana Aisha.

Malam Abdulwahab Goronyo ya ce, gwamnati tare da hadin gwiwar ma’aikatar kula da kananan hukumomi ta gudanar da ayyuka fiye da 50 da ya hada da gyare-gyaren masallatai.

Haka zalika, an gudanar da ayyuka daban-daban a karamar hukumar Rabah, inda shugaban karamar hukumar, Malam Yahaya Abdullahi Gandi ya ce, gwamnati ta gyara babban asibitin garin Rabah, inda aka sanya kayayyakin aiki da gadaje da makamantan su.

Haka kuma, gwamnatin ta gina makarantar yaki da jahilci, domin amfanin al’ummar yankin.

Daga karshe, gwamnati ta kuma gudanar da ayyukan samar da wadataccan ruwan sha tare da gyara makaranta a garin Wurno.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *