Ayyukan raya kasa: Talakawan Jigawa sun gode wa Badaru -Adamu Yellow

Tura wannan Sakon


Danjuma Labari Bolari,

Daga Gombe Wani dan asalin jihar Jigawa mazaunin Gombe, Adamu Yellow Maikifi, ya jinjina wa gwamnan jihar Jigawa, Muhammad Badaru Abubakar, bisa ayyukan ci gaba da ya shimfida a fadin jihar baki daya.

Adamu Yellow Maikifi, ya ce, su kan ‘yan jihar Jigawa duk da cewa suna zaune a wata jiha amma suna alfahari da jihar bisa yadda kwalliya ta biya kudin sabulu karkashin jagorancin gwamna Muhammad Badaru Abubakar, jihar da take gogayya da sauran jihohi a kasar nan.

Yellow ya bayyana hakan a lokacin da yake zantawa da jaridar Albishir a Gombe inda ya ce, a zaben da ke tafe na shekarar 2023 ba su da wanda yafi dacewa da su zaba sai domin takarar su na APC da gwamna Badaru ya kawo wanda sun san zai dora ayyukan madallah daga inda Badaru ya tsaya.

Ya ce, haka a zaben shugaban kasa yana ganin babu wanda yafi dacewa da ya mulki Nijeriya komai ya tafi daidai kamar Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, domin shi ne jirgin fito da zai ceto kasar nan. Adamu Yellow ya ci gaba da cewa, Bola Tinubu, ya san mulki domin yadda ya gyara jihar Legas haka zai gyara Nijeriya idan al’umma suka zabe shi, a cewarsa rashin zabar Tinubu kuskure ga ‘yan Nijeriya.

Har ila yau, ya ce, kamar zuwan shugaba Buhari ne ya samu kasar cikin wani mawuyacin halin ya saita ta haka shi ma Tinubu zai dora daga inda Buhari ya tsaya.

Ya shawarci gwamna Badaru da cewa, akwai wadansu fadamu da suka cike a jihar Jigawa wadanda ya kamata yasa a kwashe su domin amfanain al’ummar jihar.

Adamu Yellow, ya ce, fadamun sun tashi daga Atarin da Doro da Darai da Mujirga da Hantse da Harbo sabuwa da tsohuwa domin gudun afkuwar ambaliya.

Ya ce, ko jihar a Gombe da suke zama gwamna Muhammad Inuwa Yahaya ya ciyar da jihar gaba fiye da yadda ake tunani, a zaben da ke tafe ko gezau Inuwa sai ya maimaita.

Daga nan Yellow Maikifi, ya ce, duk alkawuran siyasa da gwamna Inuwa Yahaya ya dauka a shekarar 2019 ya cika su har ma ya biyo al’umma bashi wanda ba su da abin da za su saka masa da shi illa su sake zabarsa a karo na biyu, domin ya sake kawo wadansu ayyukan ci gaban

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *