Ba a kashe maciji a Machina -Saboda alakarsa da fada

Ba a kashe maciji a Machina -Saboda alakarsa da fada

Ba a kashe maciji a Machina -Saboda alakarsa da fada

Tura wannan Sakon

Masu iya magana suna cewa, “kudi da maciji, maganinsu kashewa”. Sai dai a garin Machina, fadar masarautar, a karamar hukumar Machina da ke da nisan kilo mita dari uku daga garin Damaturu, fadar gwamnatin jihar Yobe, abun ba haka yake ba. Maciji dai a garin Machina tamkar kadangare ne, babu wanda yake damuwa da shi, haka shi ma ba ya damuwa da kowa.

Maciji a Machina yana da muhimmanci kamar yadda sarkin Machina, Alhaji (Dokta) Bashir Albishir Bukar Machinama ya bayyana wa manema labarai a fadarsa da ke Machina.

Alhaji (Dokta) Bashir Albishir Bukar Machinama ya ce, gaskiya ne maciji yana daga cikin ’ya’yan masarautar Machina, kamar yadda ya fadi.

Shekaru da dama da suka shude an yi wata mata daga cikin matan sarakunan Machina wadda ta haifi tagwaye, daya daga cikin tagwayen ya kasance maciji ne, kwanaki kadan da haihuwarsu, shi wannan maciji ya ja jiki ya fice daga gidan sarautar ya koma cikin wasu manyan duwatsu da suke daf da gidan sarautar, ya yi zamansa a can.

Wannan maciji a cewar sarkin, “ya hayayyafa har ya zuwa wannan zamani da muke ciki, kuma har gobe zuri’ar wannan maciji suna tare da mu”.

Sarkin ya ci gaba da cewa, “babu mutumin da wadannan macizai suke damun sa, haka kuma muna zaune tare da su lafiya, sun kasance tamkar abin sha’awa a wurinmu”.

Sarkin ya ce, ba sa yadda a kashe ko a doki daya daga cikin wadannan macizai, haka kuma dukkan mutumin da ya kashe ko ya doki daya daga cikin wadannan macizai, ya sani, mutuwa ce makomarsa, ko ya lalace baki daya.

Wani abin sha’awa da alfahari shi ne, a duk lokacin da wani al’amari zai faru ko na farin ciki ko sabaninsa, suna ganewa daga wannan maciji, saboda kimanin mako guda kafin faruwar wannan al’amarin zai kawo ziyara cikin fada, ganinsa ke da wuya su kuma sai su dukafa da addu’a saboda rashin sanin takameman abin da ya sa ya kawo ziyara, amma dai sun san ba ya fitowa a haka kawai.

A lokutan bukukuwa shi ma yana fitowa ya yi shawagi, amma babu wanda yake wa illa.

“A lokacin da muke gabatar da wasannin al’adun gargajiya na shekara-shekara a nan Machina, mutane da dama sun yi arba da shi” a cewar sakin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *