Ba za mu koma kotu ba sai da tsaro – Lauyoyin Marafa

Ba za mu koma kotu ba sai da tsaro - Lauyoyin Marafa

Kungiya Lauyoyi

Tura wannan Sakon

Daga Shu’aibu Ibrahim Gusau

Lauyoyin Sanata Kabiru Marafa suka ki halartar kotu, inda suka ce sai alkalin alkalai ta Jihar Zamfara, Hajiya Kulu Aliyu ta ba su tabbacin tsaron lafiyarsu da rayukansu.

Daya daga cikin lauyoyin Sanatan, Misbahu Salahuddin ya bayyana hakan lokacin da yake zantawa da manema labarai a Gusau, ya kara da cewa, a ranar 17 /2/ 2022 suka halarci kotu inda wadansu matasa ‘yan bangar siyasa magoya bayan gwamnati suka yi kokarin kai wa lauyoyin Sanata Kabiru Garba Marafa hari, inda ya ce, sun kwaci kansu da kyar.

Ya kara da cewa, hakan ya sa suka dauki matakin rubuta wa Alkalin alkalai ta jihar Zamfara cewa, rayuwarsu tana cikin hadari, domin haka suna bukatar ta sauya masu wuri ko ta sama masu jami’an tsaro, domin tsaron lafiyarsu.

Sai dai ya ce, lokacin da za’a sake shiga kotun ba a ce masu komai ba, kuma Babu wata takarda da aka rubuto masu domin su san matakin da aka dauka.

Don haka za su ci gaba da sauraren ta alkalin alkalan jihar Zamfara har zuwa lokacin da za a sake shiga kotu, idan kuma babu wani mataki da ta dauka za su dauki matakin da ya dace.

A halin da ake ciki dai kotu ta sanya ranar 18 ga watan Mayu 2022 domin ci gaba da sauraron karar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *