Babbar nakasa, mutuwar-zuci -Rukayya Aliyu

Rukayya Aliyu

Tura wannan Sakon

Labari Salisu Baso,

Wata matashiya daga jihar Kaduna, Rukayya Aliyu ta bayyana cewa, nakasar zuci ita ce babbar nakasa a rayuwa.

Ta fada wa wakilinmu haka a ganawarsa da ita a babban filin wasa na kasa a lokacin bikin bude gasar wasannin nakasassu ta kasa a Abuja.

Ta kara da cewa, ba nakasassu ba ne babu amma babbar nakasa ita ce mutuwar zuciya a tsakanin nakassu, musamman masu bara, haka kuma akwai wadanda ba su da nakasar amma suna bara.

Rukayya da ta biyo tawagar jihar Kaduna a gasar wasannin, inda ta ke wasan tseren kekuna, ta yaba da kokarin gwamnati na shirya gasar a tsakanin nakassu na kasa, inda ta bayyana cewa, gasar za ta kara samar da zumunci da fahimta a tsakanin masu bukata ta musamman.

Ta kuma yi kira ga gwamnatin jihar Kaduna da ta samar da kayayyakin wasa ga nakasassu domin samar da ingantacciyar rayuwa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *