Babu abin da na sani a rayuwata sai sarauta -Dan Goruban Zazzau

Babu abin da na sani a rayuwata sai sarauta -Dan Goruban Zazzau
A kwanakin baya mai martaba Sarkin Zazzau Jakada Ahmed Nuhu Bamalli ya nada ALHAJI MUHAMMADU AMINU ZAKI a matsayin DAN GORUBAN Zazzau.Bayan kammala nadin wakilinmu da ke Zariya ISA A. ADAMU ya zanta da Dan Goruban Zazzau kan rayuwarsa da kuma yadda sarauta ta ke a rayuwarsa.
Ga yadda tattaunawarsa da wakilinmu ta kasance, — Za mu so ka bayyana ma na cikakken tarhin rayuwar ka An haife ni a shekara ta 1959, kuma iyaye na sun shaida ma ni cewar, ranar da Sarkin Zazzau Malam Jafaru ya rasu,Kamar yadda kyakkyawar al’adar al’ummar musulmi ta ke nan ganin da zarar yaro ya dan ta sa iyayensa za su sa shi a makarantar Allo, ni ma na sami wannan damar, wanda na fara da karatun Allom a makarantar Allo a Malam Allo kusa da gidanmu, makarantar Malam Adamu, bayan na ci gaba da girma sai iyaye na suka sa ni a makarantar firamare ta Nurul Huda da ke Tudun Wadan Zariya, ban kammala karatun firamare a wannan makaranta ba, sai aka yi ma ni canjin makaranta zuwa makarantar firamare ta Tudun Wadan Zariya, a lokacin ana kirar ta L.E.A Tudun Wada, na kammala wannan makaranta a shekara ta 1974.
Bayan na kammala wannan makaranta da na ambata, sai na sami shiga sakandaren gwamnati da ke birnin Zariya, wadda ake kirar tad a sunan ‘’ ALHUDA – HUDA COLLEGE’’ na shiga wannan kwalejin a shekara ta 1974 na kammala a shekara ta 1979, kammala wa ta ke da wuya, sai na sami damar shiga kwalejin kimiyya da fasaha ta gwamnatin tarayya da ke Kaduna’’ KADPOLY’’ inda na yi kwas na musamman kan yadda ake gudanar da mulkin kananan hukumomi na wata tara, na sake komawa wannan kwalen na sami takardar shaida kan yadda ake tafiyar da kananan hukumomi na shekara biyu.
Bayan na kammala wannan aiki ne, mai martaba Sarkin Zazzau marigayi Alhaji Shehu Idris ya sa aka ba ni aiki a ofishin Sarkin Ruwan Zazzau Alhaji Mahmudu Abduljalil wanda kuma a wancan lokaci, shi ne Hakimin birni Babu abin da na sani a rayuwata sai sarauta -Dan Goruban Zazzau da Kewaye, wanda na fara wannan aiki a shekara ta 1982, bayan na yi aiki da Sarkin Ruwan Zazzau sai aka yi ma ni canji zuwa ofishin Wakilin Kudu na Zazzau marigayi Alhaji Yakubu, way a keg a Salanken Zazzau Abdulkadir, na yi aiki da shi na tsawo shekara daya, sai aka yi ma ni canjin aiki zuwa majalisar karamar hukumar Zariya, inda aka tura ni bangaren tara kudaden shiga na karamar hukumar Zariya, a lokacin a na karamar hukumar Zariya baki daya, wanda zuwa yau, an cire kananan hukumomi guda tara daga tsohuwar karamar hukumar Zariya, sai aka sake mayar da ni ofishin Iyan Zazzau Muhammad Bashari Aminu a matsayi mai bayar da takardar shaida na hakin kabari da takardar shaidar haihuwa.
Bayan an kirkiro karamar hukumar Sabon gari sai aka sake yi ma ni canjin wajen aiki zuwa Maigana, a matsayin babban jami’in tara kudaden shiga na karamar hukumar Sabon gari, a lokacin gwamnan jihar Kaduna na soja Hamidu Ali aka yi ma ni ritaya daga aikin gwamnati, a na yi ma ni ritaya sai na shaida wa mai martaba Sarkin Zazzau marigayi Alhaji Shehu Idris, sai aka yi ma ni Madakin Tudun Wadan Zazzau, wanda wannan sarauta ce da mahaifi nay a rike har zuwa komawarsa ga Allah, sai aka ba ni Unguwar da mahaifi na ke kula das hi, wato Tudun Wadan Zariya ta tsakiya, ina dai Madakin Tudun Wadan Zariya, sai aka dauke ni aikin wucin gadi bayan an kirkiro karamar hukumar Soba, sai aka sake komawa da ni karamar hukumar Sabon gari, bayan na bar aiki sai na dawo gida, ina Madakin Tudun Wada, ina kuma gudanar da ayyukan ofishin Hakimin Tudun Wada.
—- Bayan an karta masarautu da kananan hukumomi da kuma gundumomi, ina aka je kuma ? Da aka kara masarautu ne sai mai martaba Sarkin Zazzau Marigayi Alhaji Shehu Idris ya nada ni Sarkin Famfon Hwaiba, wato aka raba gundumar Tudun Wada biyu, sai aka ba ni kula sashi daya,kwatsam, sai sarkin Zazzau ya ce bay a son a rika kira na Sarkin Famfon Gwaiba, ya sa aka canza zuwa Sarkin Nasarawa, ya ce daga wannan rana na koma Sarkin Nasarawa.
—– A rayuwar ka akwai tafiye – tafiye da suka kai ka wasu kasashe na kusa ko kuma na nesa ? Lallai a rayuwa tan a yi tafiye – tafiye, wanda ban san iyaka ba a ciki da wajen Nijeriya, amma batun cikin Nijeriya, babu gari babba da jihohin da ban je ba a jihohin arewacin Nijeriya, zan iya tunawa a shekara ta 1977, su na zuwa kallon sukuwar Folo a Zariya, a dalilin wani kanin Galadiman Kano, na san Galidimana mu ka yi karatu tare. Kuma tun da Allah ya hada ni da Galadiman Kano Tujjani Hashim, duk inda ake batu na sarauta a arekacin Nijeriya ko kuma za a bayar da sanda ga wani sabon sarki za mu je tare da shi,ta haka na zagaye Nijeriya ta arewa na san al’umma suka sanni, musamman, babu wani sarki da ke arewacin Nijeriya da bai sanni ba, kuma ya sanni ne a dalilin sarauta da kuma gudanar da sha’anin mulki.
—- Me za ka ce kan wannan sarauta na Dan Goruban Zazzau da mai martaba Sarkin Zazzau Jakada Ahmed Nuhu Bamalli ya tabbatar ma ka da shi ? Baa bin d azan ce ga sabon sarki Zazzau sai addu’ar samun sakayya daga mai kowa mai komi, Kuma mu na tare da shi fiye da shekara 45 dare da rana mu na tare, ko da lokacin da ya zama jakadan Nijeriya a wasu kasashe, duk lokacin day a zo Zariya mu na tare, in tafiya zai yi, tare mu ke yin tafiyan, na san lokacin da zai zo Nijeriya na san lokacin da zai Nijeriya zuwa kasashen da ya ke yin jakadanci. Kuma zan shaida ma ka cewar, sabon sarki a gaban mahaifinsa ya ganni, duk tafiye – tafiye da mahaifinsa Magajin Garin Zazzau Alhaji Nuhu Bamalli, da ni ya ke zuwa, domin mahaifi na tsohon Madakin Tudun Wada babban aminin Magajin Garin Zazzau ne Alhaji Nuhu Bamalli.
— A lokacin da mai martaba Sarkin Zazzau ke jawabi bayan nadin ku a Fadar Zazzau, ya ce, ‘’ duk cikin wadanda ya nada babu wanda ya san mulki da gogewa a mulki kamar ka, ya ka ji a lokacin day a ke furta wannan kalami a kan ka ? Nan ta ke hawaye ya fito daga ido na, domin Kalmar da ya fadi a kai na,domin a wannan rana ya bayyana wa dubban mutanen da ke Fadar Zazzau ko waye ni a fagen sanin sarauta ba a masarautar Zazzau kawai ba a arewacin Nijeriya baki daya.
A gaskiya ni a rayuwa ta babu abin da na sani ba ya ga batun yadda sarauta ta ke, na Zazzau da sauran masarautu da suke arewacin Nijeriya, saboda haka, abin da mai martaba sarki ya furta dai – dai ya furta duk wanda ya sanni ya san wannan batu, babu canji a cikinsa.
—- Yanzu me ke gaban ka ? Ai babban abin da ke gaba na shi ne batun mulki kawai, domin ka ga sarki ya nada ni, saboda sanin mulki, na fi son zuwa gidan mai unguwa in yi hira, ba gidan mai kudi ba