Babu batun hadewa da Bola Tinubu –Kwankwaso

Babu batun hadewa da Bola Tinubu –Kwankwaso

Kwankwaso

Tura wannan Sakon

Zainab Sani Shehu Kiru

Dan takarar shugabancin kasa a jam’iyyar NNPP, Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso ya karyata rade-radin da ake ta yi cewa, zai ajiye takararsa, ya mara wa Bola Ahmed Tinubu ko Atiku Abubakar baya a zaben 2023.

Kakakin yakin neman zaben na Sanata, Kwankwaso, Ladipo Johnson, ne ya karyata rade-radin cewa, dan ta takarar na tunanin mara wa wadansu ‘yan takara baya shi kuma ya hakura da ta sa.

A wata sanarwa da ya fitar a Legas a ranar Lahadi, Johnson ya ce, “Kwankwaso na cikin takarar zaben 2023. “Ban san ta yaya da kuma dalilin da ya sa mutane ke kawo wadannan labarai da hasashe ba. Kwankwaso ba zai iya ba kuma ba zai sauka domin kowa ba.”

Ya ce, Kwankwaso zai tsaya takarar shugaban kasa a shekarar 2023 har zuwa karshe yayin da ya shiga takarar tabbatar da cewa, zai kawo canjin da ake so a Nijeriya.

“Kwankwaso ba ya sasanta wa da kowa. Yana da kwazo da tarihin kwarewa da kuma kishin siyasar da zai kai Nijeriya ga tudun mun-tsira. “Dan takarar mu ba shi da dalilin ajiye takara. Akwai yakini mai karfi na cewa, zai samu nasara a zaben.

Tabbas tsere ne mai zafi, amma ya na da dama mai karfi ta samun nasara duba da yadda ya ke samun karbuwa a fadin kasar nan,” in ji shi.

Ya ce, jam’iyyar NNPP a shirye take domin gudanar da yakin neman zabe, kuma za ta ratsa kasar baki daya domin shawo kan ‘yan Nijeriya da kuma bayyana dalilan da ya sa za su goyi bayan jam’iyyar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *