Babu hanya face hanyar zaman lafiya -Shehun Borno

Shehun Borno

Shehun Borno

Tura wannan Sakon

Sani Gazas Chinade, Maiduguri

Maimartaba Shehun Borno, Dokta Abubakar Ibn Umar Garbai El-Kanemi, ya ce, babu wata hanya da ya dace abi da ta wuce hanyar zaman lafiya a jihar Borno lura da halin da jihar ta samu kanta tsawon shekaru 13 da suka gabata kan matsalolin tsaro.

Uban kasar wanda kuma shi ne shugaban majalisar Sarakuna na jihar Borno ya bayyana hakan ne a lokacin da ya karbi bakuncin tawagar hadin gwiwar Bankin Duniya da Hukumar ci gaban Arewa Maso Gabas (NEDC) a fadarsa karkashin jagorancin babbar kwararriyar ci gaban al’umma ta Bankin Duniya, Hajiya Zara Binta Goni tare da Olufunmilola Temitayo Ayoola da Maryam Maina Ma’aji Lawan da Hamza Muhammad da Dokta Francis na NEDC a Maiduguri.

Basaraken ya kuma bai wa tawagar tabbacin shirye-shirye da dukanin shugabannin gargajiya da na addini ke da shi kan duk wani aiki nagari da nufin samar da zaman lafiya da hadin kan al’umma.

Ya kuma bayyana kungiyar zaman lafiya ta Multi Sectoral Crisis Recobery Project (MCRP) da ke aiki a cikin al’ummomi a fadin jihar Borno a matsayin masu samar da zaman lafiya, hadin kan al’umma da sake hadewa waje guda.

Ya ce “Daular Kanem Borno ta fuskanci ibtila’i, jarrabawa da matsaloli da dama a tsawon shekaru fiye da 1400 da wanzuwa ta a matsayin Daula wadda kuma shi ma rikicin Boko Haram ba zai zama daban ba shi din ma cikin yardar Allah za su rabu da shi wajen ganin karshen sa.

“Ba zan manta ba akwai lokacin da Wani dan kunar bakin wake ya yi lokarin halaka ni, amma Allah ya kubutar da ni, kuma hakan ba ya nufin ba za mu iya yafewa wadanda suka yi nadamar abin da suka yi da furucinsu ba da kuma aikace, yayin da duk suka yi watsi da kungiyar kuma suka tuba.” in ji Shehun Borno.

Ya kuma yabawa Bankin Duniya da MCRP kan yadda suke taimaka wa al’ummar Borno ta hanyoyi masu kyau, tare kuma da irin jajircewa da juriya da gwamnan Jihar Babagana Umara Zulum ke yi wajen sake gina jihar musamman bisa ga Kudirin sa na sake tsugunar da al’ummomin da iftila’in masu tada kayar baya ya shafa da suka bar muhallin su na asali don zuwa hijira wasu yankunan Jihar da wasu jihohin Kasar da kuma kasashe makwabta mu.

Da take jawabi tun da farko, shugabar tawagar bankin duniya, wadda kuma babbar jami’a ce ta ci gaban al’umma ta bankin, Zara Binta Goni, ta ce ziyarar wani bangare ne na dabarun samar da zaman lafiya da hadin kan al’umma. Ta yi nuni da cewa, muhimmancin da shugabannin gargajiya da na addini suke da shi wajen samar da zaman lafiya, magance rikice-rikice da warware matsalolin ba abun jefarwa bane.

Hajiya Zara ta bayyana cewa, sarakunan gargajiya na taka muhimmiyar rawa wajen kawo sauyi da ci gaban al’umma musamman a wannan wuri na sake tsugunar da ‘yan gudun hijirar da suka dawo daga yankunan da ke fadin jihar da kuma Arewa maso Gabas .

Ta kuma zayyana yadda aka samu, tsari, ayyuka da kuma yadda za a kafa ’yan kungiyar zaman lafiya a kananan hukumomin Bama, Chibok, Damboa, Dikwa, Gwoza, Kala Balge, Mobbar, Monguno da Ngala da aka zaba bisa dabaru. “Yanzu da al’ummomin ke komawa gidajensu, ta ce, za a sake fasalin ‘yan kungiyar ta zaman lafiya tare da karfafa su don tabbatar da su masu inganci bayan an horar da su kan warware takaddama don gudanar da adalci,” in ji Zara.

Sai dai kuma ta nemi tallafi daga Basaraken a matsayin sa na uba kuma mai kula da al’umma da al’adunsu da kuma sauran shugabannin gargajiya da na addini da kuma na al’umma da su goyi bayan wannan matakin domin a samu zaman lafiya da daidaito da adalci.

Ta yi nuni da cewa za a kara horar da kungiyar a matsayin masu kula da zaman lafiya a yankunansu domin samun ingantacciyar fa’ida dangane da zamantakewa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *