Bagwai za ta tallafa wa makarantun Alkur’ani -Zangina Dangada

Zangina Dangada
Daga Ibrahim Muhammad Kano
Karamar hukumar Bagwai ta jaddada kudurinta na ci gaba da tallafa wa ci gaban makarantun Islamiyya da na Kur’ani a yankin.
Shugaban karamar hukumar, Alhaji Zangina Dangada wanda Sakataren mulki na karamar hukumar, Alhaji Abdullahi Aliyu Usman ya wakilta a wajen walimar saukar haddar Kur’ani da daliban makarantar Madinatul Ahbab Najamul Huda da ke garin Gadanya ta gudanar.
Sakataren mulki wanda shi ne ya wakilci dan majalisar tarayya mai wakiltar Bagwai da Shanono, Alhaji Yusuf Barau ya yaba wa wadanda suka kafa makarantar tare da yi masu alkawarin duba yiwuwar fiye masu fili domin samar da muhallin makarantar na din-din-din.
Sannan ya mika tallafin dan majalisar tarayya na Naira dubu 30 ga makarantar, sannan ya mika tallafin shugaban karamar hukumar Bagwai na Naira dubu 10 ga makarantar.
Sakataren mulki na Bagwai, Alhaji Abdullahi Aliyu Usman ya ce, karamar hukumar karkashin jagorancin shugaban karamar hukumar da dan majalisar su na tarayya suna bayar da gudummuwa wajen ci gaban makarantun Islamiyya da na Kur’ani a yankin wanda adadin makarantun sun kai fiye da guda 100.
Shi ma a nasa bangaren, Dagacin garin Gadanya, Alhaji Kawaji Lawan ya ba mutukar jin dadi da farin cikinsa bisa assasa makarantar da yake koyar da tarbiyya da ilimin Kur’ani a garin ya ce, za su ci gaba da kulawa da ci gaban makarantar, sannan ya ja hankalin iyaye a kan su dage sosai wajen bayar da kulawa ga ‘ya’yansu wajen raya karatun Kur’ani.
Da yake karin haske, shugaban makarantar, Malam Husaini Sheik Hamza ya ce, an kafa makarantar ne shekaru biyar da suka wuce kuma muhalli da suke wani bayan Allah ne ya ba su, su zauna Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya ce: “Wanda bai gode wa kaDan ba, ba ya gode wa da yawa, kuma wanda ba ya gode wa mutane ba ya gode wa Allah, magana da ni’imar Allah godiya ce, kuma barinsa sabo ne, kuma HaDuwa cikin jama’a rahama ce, rarraba kuma azaba ce”Shaikh Khalifa Sharif Niasee har lokacin da za su mallaki na su.
Ya yi kira ga shugaban karamar hukumar Bagwai da ‘yan majalisun su na jiha da na tarayya su taimaka masu da muhallin makarantar na din-din-din. Da yake zantawa da ‘yan jarida daya daga manyan baki da suka halarci saukar, Dokta Salisu Adam daga asibitin kashi na Dala ya ce, ya yi mutukar farin ciki da ganin yara kanana sun haddace Kur’ani da hakan ba karamin ci gaba ba ne, wannan ya nuna irin jajircewa da Malamai da mutanen garin Gadanya suke bayar wa da sai dai fatan Allah ya saka masu da alheri.
Dokta Salisu Adam Gadanya ya yi nuni da cewa, kamar yadda addini ya koyar duk cewa, idan aka bai wa mutum za a tambaye shi a kan wannan, domin haka ya kamata kowa ya fahimci cewa, sanya dansa a makaranta da zai sami ilimi da kyakkyawar tarbiyya musamman ma ya haddace Kur’ani ba karamin abu ba ne, kowane mahaifi da mahaifiya yana da muhimmanci su jajirce wajen ganin ya’yansu sun sami karatun Kur’ani da sauran ilimi.
Dokta Gadanya ya nuna gamsuwarsa bisa irin gudummuwa da al’ummar garin Gadanya suke bayar wa wajen bunkasa karatun Kur’ani tare da kira ga sauran garuruwa da ke yankin Bagwai dama sauran wurare da ba su da irin wadannan makarantu Allah ya ba su dama su assasa irin wannan iyaye, kuma kowa ya dage ya ga dansa ya sami Kur’ani kamar yadda aka gani yara a makarantar Madinatul Ahbab ta Gadanya sun samu.
Taron ya sami halartar wadansu daga iyayen kasa na masarautar Bichi da shugabannin rukunin makarantun Madinatul Ahbab na kasa.