Bai wa marayu kayan sallah, neman lada -Zahra Galadima

Zahra Galadima

Zahra Galadima

Tura wannan Sakon

Daga Danjuma Labiru Bolari Gombe

Dandalin sada Zu­munci na zauren sada Zumunta a shafin yanar gizo na ya rarrabawa marayu 100 kayan sallah a birnin Kano domin sosa masu rai.

Dandalin wanda akakafa shi tun farko domin taimakon mambobinsa da ke karamin karfi sannan su taimaka wa gajiyayyu, a makon jiya ya rarra­bawa marayu fiye da 100 kayan sallah, domin su ma su yi sallah da sabon kaya kamar kowanne mai uba.

Shugabar Dandalin ce Hajiya Fatima Zahra Galad­ima, ta shaida wa manema labarai hakan a lokacin da suka rarraba kayayyakin da suka saya ta hanyar karo-karo a tsakanin mam­bobin su, domin neman lada a wajen Ubangiji.

Hajiya Zahra Galadi­ma, ta kara da cewa, kafin su rarraba kayan sallah sun rarraba wa marayun kay­ayyakin masarufi da azumi saboda falalar watan, wan­da idan ya wuce ba lallai ba ne wani ya sake riskar sa ba.

Zauren sada zumuncin ya saba gudanar da ayyu­kan alheri a kowanne lo­kaci ba sai watan azumi ba domin ko a kwanakin baya sun gudanar da wani taro a garin Zariya, inda suka tallafawa gajiyayyu, inji Zahra Galadima.

A cewar ta suna tallafa wa matan da suke masu karamin karfi da wadanda suke rike da marayu do­min su samu sana’ar da za su yi domin su dogara da kansu.

Daga karshe, Zahra Galadima, ta yi amfani da wanan damar wajen yin kira ga masu hannu da shu­ni da dai dai kun jama’a da su dinga kulawa ko dau­kar nauyin marayu.

Hajiya Fatima Zahra Galadima

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *