Bai wa sarkin Bichi sanda, ci gaba ga masarauta -Al’ummar Masarautar

Tura wannan Sakon

Daga Jabiru Hassan

Al’umomi daban-daban daga masarautar Bichi sun taya murna ga Maimartaba sarkin Bichi, Alhaji Nasir Ado Bayero bisa bashi sandar mulki da gwamna Dokta Abdullahi Umar Ganduje ya yi ranar Asabar da ta gabata.

Mafiya yawan mutanen da suka zanta da Albishir jim kadan bayan mika sandar mulkin, sun bayyana cewa, ko shakka Babu, gwamnan jihar Kano Dokta Abdullahi Umar Ganduje ya cancanci yabo, saboda inganta sarautar gargajiya da yake yi a jiharsa tare da bai wa sarautar gargajiya muhimmanci. Alhaji Usman Dan Gwari, want jigo a kungiyar masu sana’ar kayan Gwari da nomansa ya ce “ gwamna ya cancanci yabo da girmamawa saboda kokarin da ya yi na kirkiro karin masarautu a jihar Kano, wanda hakan ta sanya jihr ta yi fice wajen kusantar da shugabanni ga al’umma musamman a wannan lokaci na bukatr gudummawar sarakunan gargajiya”.

Ya ce, a matsayinmu na ‘yan masarautar Bichi, za mu ci gaba da bayar da tamu gudummawar wajen tabbatar da cewa, ana samun nasarori na tafiyar da sarauta tare da tallafa wa masarautar Bichi wajen aiwatar da dukkanin manufofin ta duba da yadda Maimartaba Sarkin Bichi, Alhaji Nasir Ado Bayero yake da matukar burin kawo mana ci gaba a wannan masarauta tamu mai albarka.

A nasa tsokacin, mai Unguwar Zangon Dawanau da ke gundumar Dawakin Tofa, Malam Bala Adamu ya ce, maimartaba sarkin Bichi yana da kishin masarautar mu domin kowa yaga irin kokarin da yake yi wajen kawo abubuwa na ci gaban al’umma kamar fannin ilimi da dogaro da kai da kuma zaman lafiya.

Haka kuma mai unguwa Bala Adamu Zangon Dawanau ya kara da cewa” da yardar Ubangiji, masarautar Bichi za ta zamo abar misali a wannan kasa ta mu musamman ganin cewa, Maimartabajagora ne adali wanda kuma yake da basirar kawo wa al’ummarsa ci gaba mai albarka, tare da fatan Allah ya taimaki sarkin Bichi ya kuma kawo ci gaba a masarautar Bichi.

Shi ma da yake bayyana farin cikinsa, shugaban hukumar manyan makarantu, Dokta Kabir Bello Dungurawa ya fara godiya ga Ubangiji bisa ganin ranar da aka bai wa sarkin Bichi sandar mulki, sannan ya gode wa gwamna Abdullahi Umar Ganduje saboda kokarin da yake wajen kara samar da yanayi mai gamsarwa ga masarautar jihar Kano guda biyar wanda hakan ya kawo ingantaccen ci gaba a jihar kamar yadda ake gani yanzu haka.

Dokta Dungurawa ya kuma taya Maimartaba Sarkin Bichi murnar karbar sandar mulki da ya yi wanda kuma hakan zai zamo alheri ga al’ummar masarautar Bichi, musamman ta fuskar zamantakewar al’umma da kuma samar da managarcin ci gaba a yankin ta kowane fanni na rayuwa.

Wani fitaccen Malamin addinin Musulunci, Sheikh Adam Na Malam Yau ya ce, tun lokacin da gwamnatin jihar Kano ta kirkiro karin masarautu a jihar ake ganin alherin abin, duba da yadda yadda al’amura suke tafiya ta fuskar shugabancin da aiwatar da manufofin gwamnati.

Ya ce, a bangarenmu na almajirai za mu yi kokari wajen ci gaba da addu’oi na musamman ta yadda za’a ci gaba da samun ci gaba mai albarka a masarautun jihar Kano, sannan za mu kara himma wajen gudanar da addu’oi na samun dawwamammen zaman lafiya a kasa baki daya.

A karshe, dukkanin mutanen da wakilinmu ya tattaunawa da su sun sanar da cewa, gwamnatin jihar Kano bisa jagorancin gwamna Dokta Abdullahi Umar Ganduje ta samar da yanayi mai gamsarwa na zaman lafiya da karuwar arziki ta hanyar kirkiro karin masarautu domin kyautata sarautar gargajiya da bunkasa hadin kan al’umma.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *