Bala Kokani ya sama wa mazabarsa kwale kwale -Domin saukaka safara

kwale kwale

kwale kwale

Tura wannan Sakon

Musa Lemu Daga Sakkwato

Dan majalisar tarayyar APC da ke wakiltan Kebbe da Tambuwal a jihar Sakkwato, Alhaji Bala Kokani ya taimaka da jiragen kwale kwale ga gundumomi biyar da ke cikin yankinsa domin sauwakawa al’ummar yankin tafiyar da harkokin su na yau da kullum.

Kokani ya bayyana hakan ne a lokacin da yake zantawa da wakilinmu da ke Sakkwato a ranar Talatar da ta gabata. Ya ce, bayar da gudummuwar ya zama wajibi ganin yadda al’ummar yankin ke fama da wahala a lokacin daukar kayayyakin masarufi zuwa kasuwanni.

Alhaji Bala Kokani ya ce, an rarraba jiragen kwale kwale ga shugabannin al’ummar gundumomin yankin garin Kebbe da suka hada da garin Girkau, da sabon Birni da Maceri da sha Alwashi da garin Kebbe. Ya ce, an kuma mika kwale kwale ga mutanen da suka cancanta domin ci gaba da harkokinsu na yau da kullm.

Kokani ya ce, kwale kwalen ya lakume zunzurutun kudi har Naira miliyan 650, sai dauka da saukewa ga gundumomi biyar da ya lakume Naira miliyan 60, a inda aka kashe jimlar kudi Naira miliyan 920.

Bala Kokani ya kasance gwarzon dan siyasa kazalika zakaran gwajin dafi da ya bautawa jiharsa tun daga matakin matakin karamar hukuma a inda ya kasance shugaban karamar hukumar Kebbe sau biyu. Kazalika kwamishinan kudi da tsare-tsaren tattalin arzikin jihar Sakkwato, inda a yanzu ya kasance dan majalisar tarayya da ke wakiltar Kebbe da Tambuwal.

A lokacin da wakilinmu ya zanta da al’ummar da suka amfana da taimakon sun nuna matukar jin dadin su da godiya ga dan majalisar da taimakawa da ya yi a gare su, tare da yi masa fatan alheri.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *