Ban yanke shawara kan takarar shugaban kasa ba – Osinbajo

Ban yanke shawara kan takarar shugaban kasa ba – Osinbajo
Daga Muhammad Mustapha Abdullahi
Ofishin Mataimakin Shugaban Najeriya Farfesa Yemi Osinbajo ya ce sam ba shi da masaniya kan hotunan da ke yawo a wadansu sassan kasar na bayyana aniyar tsayawa takarar shugaban kasa a 2023.
Cikin wata sanarwa da mai magana da yawun mataimakin shugaban, Laolu Akande ya fitar, ofishin ya ce, Osinbajo bai yanke shawarar tsayawa takara ba tukuna.
“Ofishin mataimakin shugaban kasa ba shi da hannu ko kadan wajen rarraba fastar takarar 2023 walau a kan tituna ko kuma a intanet da shafukan zumunta,” a cewar sanarwar.
“Wannan yunkurin karkatar da hankula ne daga shugabancin kasarmu wanda ba a bukata a yanzu.” Kwana biyu da suka gabata ne wasu hotuna suka karade biranen Kano da Abuja dauke da Yemi Osinbajo da gwmnan Kano Abdullahi Ganduje a matsayin dan takarar shugaban kasa da mataimakinsa.