Bankade: Kamfanoni na saye kayan abinci zuwa kasashen Asiya

Al­haji Aminu Muhammad S.Doka

Tura wannan Sakon

Daga Ibrahim Muhammad Kano

An ja hankalin gwamnatin kasar nan da ta jihar Kano, a kan lallai ta dauki kwakkwaran mataki na da­katar da wadansu masu say­en kayan abinci nau’ukan dawa da gero da masara da wake da wadansu kamfano­ni suke fakewa da sayawa majalisar Dinkin Duniya domin bai wa ‘yan gudun hijira, suna fitarwa ka­sashen Asiya da bana suka sami rashin kaiwar amfanin gona sakamakon ambali­yar ruwa suna sayarwa, da hakan zai jefa kasar nan a mawuyacin hali, muddin aka yi sake ba’a dauki mat­akin dakatarwa ba.

Jigo a kasuwar hatsi ta Duniya ta Dawanau, Al­haji Aminu Muhammad S.Doka ya yi kiran domin ankarar da gwamnati domin kada karancin kayan abinci da ta’azzarar tsadar sa ya addabi kasar nan, sakama­kon barazanar fari da za’a iya fuskanta saboda rashin kaiwar damuna a bana.

Ya ce, janyewar ruwa da aka samu zai haifar da mat­sala gagarumi, wajen sa­mun amfanin gona, saboda akwai wadanda ba za su kai ba, kuma yanzu da aka sami dawowar ruwan sama ak­wai wadansu kayan da zai lalace, saboda ruwa zai taba su.

Kuma tun yanzu far­ashin kaya da ake sa ran saukowa kasa, har an samu masara ta dawo N12,500. gero N14,000 amma yanzu gero ya doshi N20,500,00 Masara N18,000 abin ak­wai babbar matsala, wanda yanzu ma, ana cikin kaka kenan, wanda wadansu am­fanin ma bai soma zuwa ba.

Ya ce, ya kamata huku­momi lallai su saka ido a kan harkar kayan gona, sa­boda ana yakin sunkuru na saye kayan amfanin gona, ana kai wa waje alhali nan bai wadaci kasa ba.

Idan har ba’a dauki mataki ba Gero da Dawa da Masara sai sun kai N40,000.

Ya ce, akwai kamfanoni da suke shigowa suna sayen ridi da citta da kashu da zobo da gyada da sauran nau’ukan kayan gona da yake bana amfanin yau da kullum ba ne a kasar nan, yanzu suna fakewa da wan­nan suna sayen gero da dawa da masara da wake wanda duk fita za su yi da su waje, kowane kamfani akwai adadin wadansu za su sayi tan dubu 10 wadansu, 20 wadansu 15 suna nan kamfanoni da dama suna turo yaran su kai tsaye tun daga Legas, kuma basa zuwa yankin kasuwar Dawanau kar a gani, suna zuwa Kasuwanin kauye suna saye suna dorawa a tireloli zuwa Legas.

Alhaji Aminu ya ce, su sun san a tarihi Gero baya zuwa Legas in aka dora shi sai dai a kai Nijar, Mali, Burkina Faso, wanda dama suna zuwa su saya,yanzu kuma Gero ya juya ana kaiwa Legas daga nan jirgi za’a dorawa zuwa kasashen Indiya da sauran kasashe a yankin Asiya, wannan zai shafi abinci a kasarnan in har Gwamnati bata dauki mataki kan wannan ba, za’a sami gagarumar matsala za’a sami babban gibi a harka abinci a wannan shekara.

Ya yi nuni da cewa, yakamata Gwam­nati ta dauki mataki na yin bincike domin gano kamfanonin ta gano gero da dawa da masara da wake da suke saya ina za su kai, me za su yi da shi. Ya kara da cewa, sun san a baya gwamnati na sayen kayan am­fanin gona ta adana, idan lokaci ya yi kaya ya janye, ta fito da shi yanda al’umma za su amfana, wadannan matakan su yaka­mata gwamnati ta dauka na dawo da sayen amfanin gona in lokacin bukata ya yi a fito a sayarwa al’umma.

Alhaji Aminu Muhammad ya ce, yaka­mata gwamnati ta yi kyakkyawan bincike dan a dakile a hana kamfanoni da suke shigowa suna sayen kayan abincin, musam­man dawa, gero, masara da wake, kuma a lura suna fakewa da majalisar Dinkin Du niya kamar ana saya ne dan kaiwa yan gu­dun hijira tallafi na abinci,amma a zahiri ba haka bane.

Ya ce, ya sanar da kungiyar kasuwar Dawanau da jami’an tsaro kuma jama’a su dauki matakin sanar da hukumomi domin a farka kafin a makara.

Alhaji Aminu Muhammad wanda yana daga yan takara da ke neman zama shuga­bancin kungiyar kasuwar Dawanau domin kai kasuwar matsayin amsa sunanta ta ka­suwar Duniya wanda har yanzu a zahirin ta ba ta kai wannan matsayi ba.

Ya ce, suna da gudummuwa da za su bayar domin bunkasa kasuwar da ‘yan ka­suwar ta samar da hanyoyi a cikinta da za­manantar da saye da sayarwa wanda in aka ingantasu za su taimaka.

Yanzu haka duk shekara ana yin kasu­wanci na ridi na sama da Naira biliyan 100 amma in akace Gwamnati ta bada alkalu­ma na ridi da ake fita da shi daga kasuwar Dawanau ba za ta iya ba.

Ya ce, zai tabbatar da sanin kididdigar kaya da ake fitarwa kullum na kowane irin kayan abinci a kasuwar domin ba karamin hada-hada ake a cikinta ba na kayan gona, wannan ya bashi sha’awar ya fito dan dora kasuwar akan zamani da zaka iya sayarda kaya a duk Duniya daga inda kake a ka­suwar.

Alhaji Aminu Muhammad yace tunanin takarar ta yan Kasuwar ce da suka.nemi yayi, duba da gudummuwa daya bayar a lokacinda ya zama Sakataren kasuwar dan haka mutane, sukace lallai ya fito neman Shugabancinta.

Alhaji Aminu Muhammad S.Doka yace burinsa kasuwar Dawanau ta juya Kan yin Kasuwanci na zamani da kuma tabbatar da bin duk wata doka da oda ta gwamnati wajen fita da shigowa da kayan abinci a bai wa kaya tsaro a kungiyar, domin haka suna bukatar goyon bayan ‘yan kasuwar Dawa­nau.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *