Bankuna, ku kiyayi bai wa Tambuwal bashi –APC

Musa Lemu Daga Sakkwato
An shawarci bankunan da ke fadin tarayyar Nijeriya da kada su kuskura su bayar da bashin ko sisin kwabo ga gwamnatin jihar Sakkwato da take yunkurin karbowa daga bakunan domin tsira da mutuncinsu.
A yayin ganawa da taron manema labarai a Sakkwato ranar Talatar da ta gabata.
Shugaban jam’iyyar APC na jihar, Alhaji Isa Sadik Achida ya ce, bayar da shawarar ya zama wajibi hana al’ummar shiga sarkakiyar talauci da tulun bashi.
A nan ‘yan majalisar dokokin jihar sun taka rawar gani wajen nuna kin amincewarsu na karbo bashin daga bankunan.
A saboda haka jam’iyyar APC ta jinjina wa ‘yan majalisar tare da nuna goyon bayansu a kan dagewarsu na kin amincewa.
Alhaji Isa Sadik Achida ya ce, ana iya tuna cewa, ‘yan majalisar sun taba amincewa da karbar bashi na zunzurutun kudi har Naira biliyan 89 da ba a taba tsinana komai da kudaden ba ga al’ummar jihar.
Daya juya ta fuskar kasafin kudin shekarar 2023, shugaban jam’iyyar ya ce, kasafin kudin da gwamna Aminu Waziri Tambuwal ya gabatar a gaban majalisar dokokin jihar bai yi bayani ba ta yadda za su fahimci ina aka dosa ganin cewa, ba a bayyana ayyukan a zo a gani a cikin kasafin kudin ba, illa kawai labewa ne da guzuma ana harbin karsana.
Sadik Achida ya ce, APC ta gano wadansu badakala na ayyukan da aka gudanar a jihar ana ninka kudedensu ne ninkin ba ninki a inda ya bayar da misalin aikin hanyar da aka bayar wanda ya taso daga garin Dogon Daji zuwa Sabawa a kan kudi Naira miliyan 600 a inda daga baya aka nunka kudin zuwa naira biliyan daya.
Daga karshe, ya ce, tankunan samar da ruwan sha ga al’ummar jihar da gwamnatin ta gina sun kasance baba rodo, domin ba wanda ke aiki harkar ilimi ya nakasa ba magunguna asibitoci ba hanyoyi a yankunan karkara a inda aka yi watsi da ire-iren muhimman ayyuka aka fuskanci samar da motocin hawa ga kwamishinonin jihar da masu bayar da shawarwari su ne ‘yan lele.