Barca ta Baiwa Ferran Riga Mai Lamba 19

Tura wannan Sakon

Wasanni

Kungiyar Barcelona ta bai wa sabon dan wasan da ta dauka daga Manchester City a Janairu, Ferran Torres riga mai lamba 19.

 Tuni kungiyar ta kammala yi wa dan kwallon rijistar buga wasannin gasar Sifaniya, zai iya fafatawa da Real Madrid a wasan daf da karshe a Super Cup ranar Laraba. Ya kuma karbi riga mai lamba 19 a hannun Sergio Aguero wanda ya yi ritaya, sakamakon rashin lafiya ta kasa yin numfashi yadda ya kamata.

Wadanda suka sa rigar kafin Aguero sun hada da Juan Antonio Pizzi (1996-98) da Patrick Kluivert (1998-99) da kuma Leo Messi (daga Janairun 2006 zuwa 2008).

Shima Martin Braithwaite, mai amfani da lamba 12 a yanzu ya fara da lamba 19 a farkon zuwansa Camp Nou. Sauran ‘yan wasan Barca da suka yi amfani da lamba 19 sun hada da Dani (1999-03) da Maxwell (2009-12) da Sandro (2015- 16) da Lucas Digne (2016-18) da dai sauransu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *