Barca ta dauki dan wasan Chelsea, Christensen

Barca ta dauki dan wasan Chelsea, Christensen

Christensen

Tura wannan Sakon

Barcelona ta sanar da daukar Andreas Christensen daga Chelsea, bayan da kwantiraginsa ya kare a Stamford Bridge a karshen watan Yuni.

Christensen ya amince da kunshin yarjejeniyar kaka hudu da dora farashin yuro miliyan 500 ga duk kungiyar da ke son daukarsa, idan wa’adinsa bai kare ba a Camp Nou. Christensen dan kwallon tawagar Denmark ya zama na biyu da Barca ta dauka a bana, bayan Franck Kessie da ta sanar da daukarsa ranar Litinin daga AC Milan.

Dan kwallon ya koma Chelsea daga Brondby a 2012, wanda kaka biyu tsakani ya fara taka mata leda a matakin kwararren dan wasa a Blues.

Chelsea ta bayar da aron dan wasan kaka biyu ga Borussia Monchengladbach, da ya koma Stamford Bridge sai ya nuna kansa. Ya buga wa kungiyar Stamford Bridge wasa 167 har da 26 da ya yi a kakar da ta wuce da cin kwallo hudu.

Dan kwallon ya lashe Champions League da Europa League da Club World Cup da kuma UEFA Super Cup a wasannin da ya yi wa kungiyar Stamford Bridge. Haka kuma Chelsea ta yi nasarar cin wasa 92 a karawar da Christensen ya buga mata.

Bayan da Barcelona ta kammala daukar Christensen da Kessie, kungiyar za ta mayar da hankali kan zawarcin Raphinha na Leeds United.

Haka kuma Barcelona na tattaunawa da Ousmane Dembele kan tsawaita zamansa a Camp Nou, bayan da yarjejeniyar dan kwallon tawagar Faransa ta kare a kungiyar. Tuni dai Manchester United ke ta kokarin ganin ta kammala sayen dan wasan Barcelona, Frenkie de Jong kafin fara kakar bana da za a yi a cikin watan Agusta.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *