Barca ta gabatar da Alves gaban magoya-baya

Dani Alves

Tura wannan Sakon

Kungiyar Barcelona za ta gabatar da Dani Alves a gaban magoya baya a matakin dan wasa ran Laraba, sannan ya gana da ‘yan jarida a Camp Nou.

Ranar Juma’a Barcelona ta tabbatar da kulla yarjejeniya daukar tsohon dan wasan nata. Tuni kuma likitoci suka kammala auna koshin lafiyar dan kwallon tawagar Brazil ranar Litinin. An amince ya fara atisaye ranar Litinin, sai dai ba zai buga wa Barcelona gasa ba har sai a watan Janairun 2022.

Yadda aka tsara gabatar da Dani Alves gaban magoya baya ranar Laraba 12.30 na rana za a bude kofofin filin wasa na Camp Nou.

2.00 na rana za a gabatar da Dani Albes a cikin filin wasa na Camp Nou pitch 3.00 na yammaci Dani Alves zai gana da ‘yan jarida Albes mai shekara 38 wanda ya lashe manyan gasa tara a Barca da Jubentus da Paris St-Germain, zai koma kulob ɗin na Spain a kyauta don kammala wasannin gasar 2021-22.

Ɗan ƙasar Brazil ɗin ya shafe shekara takwas a Barca daga 2008 zuwa 2016, inda ya lashe La Liga shida da Zakarun Turai uku da kuma Copa del Rey huɗu. Ƙungiyar ta siffanta shi da “ɗan wasan baya na gefen dama mafi ƙwarewa a tarihin Barca” cikin wata sanarwa a shafinta.

Tun farko Barca ta fasa ɗaukar Alves, amma sabon mai horarwa Dabi ya nuna sha’awar dawo da shi tawagar domin taimaka mata dawowa kan ganiya. A watan Satumba aka dakatar da kwantiraginsa a ƙungiyar Sao Paulo sakamakon rikici kan albashinsa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *