Barca ta sanya Laliga asarar euro miliyan 892

Barca ta sanya Laliga asarar euro miliyan 892

Spain Soccer La Liga

Tura wannan Sakon

Hukumar kula da gasar La Liga ta kasar Spain ta sanar da tafka asarar kudin da ya kai euro miliyan 892 a kakar da ta gabata ta shekarar 2020-2021, yayin da ta bayyana kungiyar Barcelona a matsayin wadda tayi sanadiyar asarar sama da rabin kudin.

Hukumar tace rashin kokarin kungiyar Barcelona a kakar da ta gabata ta sanya asarar kashi 56 na kudaden da ya dace ta samu saboda yadda mutane suka kauracewa zuwa kallon wasannin ta saboda rashin kokari.

Rashin sayan karin ‘yan wasa da matsowa da yadda kafofin talabijin ke nuna wasannin gasar La Liga kai tsaye da kuma asarar kudaden talla na daga cikin dalilan tafka asarar. Kungiyoyin dake La Liga sun bayyana samun kudaden harajin da ya kai sama da Dala biliyan 4 a kakar da ta gabata, amma kuma hakan ya nuna raguwar sama da kashi 24 na kudaden da aka samu a shekarar 2019 zuwa 2020 duk da matsalar annobar korona da aka samu.

Hukumar tace wannan shine karo na farko da aka samu irin wannan asarar tun daga shekarar 2012, sai dai Hukumar tace tana fatar ganin ta farfado nan da shekaru 2 masu zuwa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *