Barcelona za ta sayi Firmino daga Liberpool

Dan wasan gaba na Brazil da ke taka leda da kungiyar kwallon kafa ta Liberpool Roberto Firmino ya zura kwallo a wasansa na karshe da ya dokawa kungiyar jiya lahadi wanda ta yi canjaras kwallaye 4 da 4 tsakaninta da Southampton wadda ta kammala gasar a matsayin ta karshe a teburi.
A karshen wannan kaka ne dai Firmino zai raba gari da Liberpool sakamakon karewar da kwantiraginsa zai yo a watan Yuni ba kuma tare da sabuntawa ba, daga kungiyar wadda ke ganin mugun koma baya a wannan kaka.
Akwai dai jita-jitar da ke alakanta Firmino da komawa Barcelona kamar yadda Daily Mail da Marca a Spain suka bayyana cewa tuni kungiyar ta Catalonia ta sanya dan wasan na Brazil a sahun cefanen da ke son yi karshen kaka.
Firmino wanda ya shafe shekaru 8 a Liberpool tun gabanin karewar kwantiraginsa, ya rika fuskantar matsalar zaman benci karkashin jagorancin Jurgen Klopp inda ma har wasu jita-jita a baya suka bayyana yiwuwar sayar da shi gabanin karewar kwantiragin nasa.
A bangare guda, itama kungiyar ta Barcelona duk da nasararta ta lashe kofin gasar La liga har yanzu ta na bukatar samar da wasu gyare-gyare don cike gibin da ta ke da shi wanda ya hadddasa mata mummunar ficewa daga gasar zakarun Turai a kakar da muka yi bankwana da ita.