Batun tsaron tasoshin mota, damuwar NURTW -Dan Simol

NURTW
Isa A. Adamu Daga Zariya
Saboda kawo karshen matsalolin tsaro da ta zama ruwan dare a wasu jihohin arewacin Nijeriya, yanzu haka kungiyar direbobin motocin haya ta kasa [ NURTW ] reshen jihar Kaduna, ta tashi tsaye na ganin ta samar da cikakken tsaro fiye da yadda ta sa a baya a daukacin tasoshin mota da suke kananan hukumomin jihar Kaduna 23.
Mataimakin ma’aji na wannan kungiya Alhaji Mustafa Lawal wanda aka fi sani da Dan Simol ya bayyana kaha, a lokacin da ya zanta da wakilinmu a Zariya, kan matakan da wannan kungiya ke dauka domin kara samar da tsaro da kuma kare mutunci da lafiyar duk wani ko wata da ta shiga ko wace tashar mota da ke kananan hukumomin jihar.
Alhaji Mustafa Dan Simo ya ci gaba da cewar, tun a shekarun da suka gabata, shugabannin kungiyar na jihar Kaduna, inda aka sa wasu ma su sa ido ga duk mai shiga tashoshin mota, wanda wannan sabanin jami’an kungiyar ne da suke sa unifom, wato kayan kungiya,sa wadannan mutane, a cewarsa, yay i matukar tallafa wa wajen kara samar da tsaro a tasoshin mota da suke jihar Kaduna.
Ya ci gaba da cewar, sun sami nasarori ma su yawan gaske na yadda wadannan jami’an tsaro na sirri da suke yin gilmayya a cikin tasoshin mota sun kama wasu da ba su yadda da mururinsu ba a harabar tasha, da in an tuhume su, a karshe, sai ka ga ashe bata gari ne ke neman inda za su fake domin aiwatar da muggan ayyukansu.
Wannan matakin sa jami’an tsaro a cikin tasoshin mota, kamar yadda Alhaji Dan Simol ya shaida wa wakilinmu, ya sa ‘jami’an ‘yan sanda sun jinjina wa kungiyar [ NURTW ], na tsare – tsaren da ta ke yi, na kare faruwar muggan ayyuka da ‘yan baya – ga- dangi ke aiwatarwa, tun kafin ma su aiwatar.
Sauran matakan da suke dauka domin tabbatar da tsaroa ciki da kuma gefen tasoshin mota, kamar yadda mataimakin ma’ajin na wannan kungiya Alhaji Mustafa Dan Simol ya shaida wa wakilinmu sun hada da gudanar da binciken da suka dace ga duk wani fasinja da ya shiga tasha da wata jaka ko kuma kunshin wani abu da ba su yadda da shi ba, inda a cikin natsuwa, su kan nemi mai buhun ya yi bayanin abubuwanda suke cikin jakarsa ko kuma wani kunshi da ya tare da shi, wannan ma, a cewarsa, sun gano matsaloli da dama daga wadanda ke shiga tasha, domin shiga motoci.
A dai zantawarsa da wakilinmu, ya ce, da zarar sun sami wani ko kuma wasu da kayayyakin da za su iya kawo matsala ga al’umma da suke shiga tashoshin mota a jihar Kaduna, su kan mika wanda suka damke ga rundunar ‘yan sanda, daga nan kuma, sai su dauki matakan da suka dace ga wanda suka kama.
A karshe, Alhaji Mustafa Lawal Dan Simol, ya bayyana tsaron da ake samu a tasoshin mota na jihar Kaduna daga kyakkywar shugabancin da shugaban kungiyar [NURTW ] na jihar Kaduna Alhaji Aliyu Tanimu Zariya ke yi, na ako wane lokaci, babban tunaninsa shi ne samar da yana yin tsaro ga fasunjojin da suke shiga tasoshin domin tafiye – tafiye zuwa sassan Nijeriya daga jihar Kaduna da kuma ganin an samar da motoci ma su inganci ga matafiya.