Bauchi ta dauki nauyin jiyyar Malama Asabe -Wadda aka nema wa taimako

Malama Asabe
Jamilu Barau daga Bauchi
Gwamna Abdulkadir Muhammad ta dauki nauyin wata baiwar Allah datake fama da matsalar jinya Wanda takici taki cinyewa gashi marasa karfine basuda komai ya kare a hannunsu.
Bayan gani da Kwamishinan Mata ta jihar Bauchi Hajiya Hajara Gidado a kafar sadarwa na yanar Gizo ba ta iya bacci ba cikin daren ta bayar da umarni lallai aka kirani na kira yan’uwan matan domin gwamanti ta taimaka masu.
Cikin ikon Allah ta yi tattaki tunda ga Bauchi ta je karamar Hukumar Katagum kauyen Tsumamaro bisa yadda da amincewar Uwargidan gwamna Hajiya Aisha Bala Muhammad wadda a yanzu haka nan take kwamishiniyar mata ta jiha ta dauki Malama Asabe zuwa asibitin kwararru na jiha da ke Bauchi domin ba ta kulawa ta musamman kyauta.
Tabbas Hajiya Hajara Gidado dole mujinjina miki bisa gagarumar gudumawar da kika bayar na gaggawa domin kawo mata dauki karakashin amincewar uwar marayu, Hajiya Aisha Bala Muhammad Abdulkadir.
Tabbas kafa ta Social Media tana bayar da gudumawa matuka wajen isar da sakonni yadda ya kamata.
Muna kara Godiya wa al’ummah ma’abota kafa ta Social Media na irin gudumawa da kuka bayar, wajen yada wannan al’amari har akai ga mahukunta sun gani sun kuma dauki mataki.
Wadanda suka bayar da gudumawa ta kudi ta banki suma Allah ya saka masu da alheri an samu kudi ya kai kimanin 65,000 Allah ya bar zumunci yan’uwa da abokan gwagwarmaya Allah yakara dafawa wa gwamantin jihar Bauchi, karkashin jagorancin gwamna Bala Muhammad Abdulkadir.